'Yadda Bello Turji Ke Nadawa da Sauke Dagatai a Sokoto Lokacin da Ya So'
- Rahotanni sun tabbatar da cewa dan ta'adda, Bello Turji shi ke iko da mafi yawan ƙauyuka a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya
- Shugaban karamar hukumar Isa, Alhaji Sharifu Kamarawa shi ya tabbatar da haka ga ƙaramin Ministan tsaro, Bello Matawalle
- Kamarawa ya ce dan ta'addan shi ke saukewa da kuma nada wasu daga cikin dagatai a mafi yawan ƙauyuka a jihar ta Sokoto
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Shugaban karamar hukuma a jihar Sokoto ya tabbatar da cewa har yanzu wasu yankuna na karkashin ikon yan ta'adda.
Shugaban karamar hukumar Isa a jihar, Alhaji Sharifu Kamarawa shi ya tabbatar da haka ga karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Sokoto: An gano yadda Turji ke ikonsa
Daily Trust ta ruwaito Kamarawa na cewa dan ta'adda, Bello Turji yana saukewa da kuma daura dagatai a kauyuka.
Hon. Kamarawa ya ce Gabashin Isa an fi samun matsala inda yan ta'adda ke da iko sosai a yankin.
Hakan ya biyo bayan ziyarar karamin Ministan tsaro jihar Sokoto a kokarin dakile yan ta'addan da suka addabi al'umma.
Yadda Turji ke nadi da sauke dagatai
"A nan garin Isa muna zaune lafiya amma a Gabashin Isa har yanzu yan bindiga ke da iko inda suke saukewa da nadin dagatai."
"Mu na rokon jami'an sojoji a sansanin Kagara su kawo dauki a wadannan wurare, a baya muna shi kafin aka dauke shi."
- Hon. Kamarawa
Hon. Kamarawa ya ce tun bayan kisan rikakken dan ta'adda, Halilu Sububu, an dan samu sauki kan hare-haren yan bindiga a yankunan inda ya ce mutane suna yin harkokinsu.
Gwamnatin Sokoto ta magantu kan Bello Turji
Mun ba ku labarin cewa bayan ganin sabon bidiyon dan ta'adda, Bello Turji, gwamnatin Sokoto ta yi magana kan dalilin aika-aikar.
Gwamnatin Sokoto ta ce Turji ya rikide ne saboda ganin shirin karar da su da Gwamna Ahmed Aliyu ke yi.
Hakan ya biyo bayan fitar da wani sabon bidiyo da kasurgumin dmà ta'adda, Bello Turji ya yi a ranar Laraba 4 ga watan Satumbar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng