Tsadar Ta Yi Yawa: TUC Ta Fadawa Tinubu Farashin da Take So Ya Mayar da Litar Fetur

Tsadar Ta Yi Yawa: TUC Ta Fadawa Tinubu Farashin da Take So Ya Mayar da Litar Fetur

  • Kungiyar ‘yan kwadago ta TUC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da farashin fetur kamar yadda yake a watan Yunin 2023
  • A wani taron manema labarai a Abuja, kungiyar TUC ta ce ba wai iya mayar da fetur farashin shekarar 2023 ba, ana so ya yi kasa da haka
  • Shugaban TUC, Festus Osifo ya kuma nemi gwamnatin tarayya da ta rika sayarwa matatar Dangote dala a kan N1000 maimakon N1600

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kwadago ta TUC ta bukaci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta dawo da farashin man fetur kamar yadda yake a watan Yunin 2023.

Shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo ya ce ba wai suna neman a mayar da farashin man yadda yake a baya kadai ba, suna so ne farashin ya sauka kasa.

Kara karanta wannan

'A dawo mana da kudinmu': Ƴan kasuwa sun hurowa NNPCL wuta bayan kara kudin mai

Kungiyar TUC ta yi magana kan tsadar man fetur da ake fama da ita a Najeriya
Kungiyar TUC ta nemi gwamnatin tarayya ta dawo da farashin fetur zuwa kasa da N450. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

"A dawo da fetur kasa da N50' - TUC

A wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, Chanels TV ta ruwaito Festus Osifo ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Muna son farashin fetur ya yi kasa da yadda yake a da; ba wai a dawo da farashin ba, muna so ne ya sauka kasa da farashin."

Ya roki gwamnati da ta karya farashin da take ba Dangote dala zuwa $1/N1,000 sabanin 1/N1,600 da ake canja dala zuwa Naira a yanzu.

"Shawarar da muke bayarwa ita ce gwamnatin tarayya ta dawo da farashin fetur kamar yadda yake a watan Yunin bara,"

- Shugaban na TUC.

Tun a watan Mayun 2023, kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya kara farashin fetur daga N184 a Legas zuwa N998. An ce farashin litar fetur ya kai N450 a watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin fetur, PETROAN ta fadawa Dangote matakin da ya kamata ya dauka

TUC ta magantu kan samuwar fetur

Shugaban kungiyar TUC ya kuma yi tsokaci game da samuwar mai da kuma wadatuwar shi ga 'yan kasar yana mai cewa:

"Muna son gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NMDPRA da ta bai wa duk 'yan kasuwa lasisin sayen mai daga matatar Dangote."

Osifo ya ce ya kamata NNPCL ta nemo tataccen mai daga wasu wurare idan har matatar Dangote ba za ta iya biyan bukatun ‘yan Najeriya na yau da kullum ba.

NLC ta soki NNPCL saboda karin kudin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta NLC ta yi Allah wadai da matakin da NNPCL ta dauka na kara farashin mai daga N897 zuwa N1,030 a wasu wurare.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi gaggawar janye karin da ta yi inda ya ce babu abin da ta iya sai karin kudi ba tare da duba halin da kasar ke ciki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.