Manyan jiragen ruwa 35 dauke da tataccen man fetir da kayan abinci sun nufo Najeriya

Manyan jiragen ruwa 35 dauke da tataccen man fetir da kayan abinci sun nufo Najeriya

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, NPA, ta sanar da manya manyan jiragen ruwa guda Talatin da biyar, 35 sun nufo Najeriya dauke da tataccen man fetir da kayayyakin abinci da dama.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito ana sa ran daga yanzu jiragen zasu fara sauka a tashoshin jiragen ruwa guda biyu dake jihar Legas, da suka hada da tashar Apapa da tashar tsibirin Tin Can.

KU KARANTA: Bahallatsar tsige Saraki: Sanatocin PDP sun tare a Abuja don su ba Saraki kariya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jiragen danakaro da yawansu ya kaia guda 35 zasu fara isowa Najeriya tun daga ranar 3 ga watan Agusta zuwa ranar 22 ga watan Agusta.

Manyan jiragen ruwa 35 dauke da tataccen man fetir da kayan abinci sun nufo Najeriya

Jirgi

NPA, tace daga ciki jiragen dankaro 35 da ake tsimayi, guda goma sha hudu daga cikinsu na dauke da tataccen man fetir ne, yayin da sauran guda ashirin da daya ke makare da danyen kifi, acca, kayan karafa, siga, manja, taki, man gas da sundukai da dama.

Haka zalika hukumar NPA, tace akwai wasu jirage guda goma sha daya da suka riga suka iso tashoshin jiragen ruwan Najeriya, wanda suke jira a saukesu, dauke da kayan taki, mai, da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel