'A Dawo Mana da Kudinmu': Ƴan Kasuwa Sun Hurowa NNPCL Wuta bayan Kara Kudin Mai

'A Dawo Mana da Kudinmu': Ƴan Kasuwa Sun Hurowa NNPCL Wuta bayan Kara Kudin Mai

  • Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta zargi NNPCL da kin sayarwa 'ya'yanta da man fetur a tsohon farashin da suka biyata kudi
  • IPMAN ta bukaci kamfanin NNPCL da ya sayar mata da fetur a farashin da matatar Dangote ta bayar ko ya mayar masu da kudinsu
  • Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Shettima ya ce watanni uku kenan NNPCL ya rikewa 'yan kungiyar kudi kuma ya hanasu mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN) ta kunnowa kamfanin man Najeriya (NNPCL) wuta awanni bayan ya kara kudin da yake sayar masu da fetur.

Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Shettima ya bukaci NNPC da ya sayar wa ‘yan kungiyarsu man fetur a farashin da matatar Dangote ke bayarwa.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin fetur, PETROAN ta fadawa Dangote matakin da ya kamata ya dauka

IPMAN ta yi magana kan farashin da NNPCL ke sayar mata da man fetur
IPMAN ta nemi NNPCL ya sayar mata da mai a tsohon farashi ko ya mayar mata da kudinta. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

"NNPCL ya dawo mana da kudinmu" IPMAN

A yayin tattaunawa da Channels TV a ranar Alhamis, Shettima ya kuma bukaci NNPCL ya mayarwa 'yan kungiyar kudaden da suke binsa wanda ya rike tsawon watanni uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa tsawaita jinkirin dawo da kudin ya sanya 'yan kasuwar man fetur sun shiga mawuyacin hali, inda ya bukaci NNPCL da ta dauki matakin gaggawa.

“Babban kalubalenmu a yanzu shi ne, mu na da kudi a hannun NNPCL da har yanzu bai biyamu ba, kuma kamfanin ya karbi fetur a kasa da N900 daga matatar Dangote."
“A halin yanzu, kudin mu suna hannun su (NNPCL) kusan watanni uku kenan.

- Abubakar Shettima.

IPMAN ta gargadi NNPCL kan farashi

Shugaban IPMAN na kasa ya ce a yanzu sun yanke shawarar cewa NNPCL ya mayar masu da kudinsu idan har ba zai sayar masu da mai a farashin da ya saya daga Dangote ba.

Kara karanta wannan

Bayan sayen fetur da sauki, yan kasuwa sun zargi NNPCL da tsuga masu farashi

“Amma da sauye-sauyen da aka samu a baya-bayan nan, mun bukaci su sayar mana da mai a farashin Dangote ko kuma su dawo mana da kudadenmu.
"Wannan shi ne halin da ake ciki yanzu kuma shi ne babban dalilin da ya jawo karancin man. Amma tun a jiya muka fara tattaunawa da su."

A cewarsa, NNPCL ya umurci ‘yan kungiyar IPMAN da su sayi fetur a hannunsa a kan N1,010 a Legas, N1,045 a Calabar, N1,050 a Fatakwal da N1,040 a Warri.

IPMAN ta soki NNPCL kan tsawwala kudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Shettima ya zargi kamfanin NNPCL da yi masu shigo-shigo ba zurfi kan farashin fetur.

Abubakar Shettima ya ce kamfanin NNPCL na sayar masu da kowace lita a kan N1,010 duk da ya na sayo shi a kan N800 – N900 daga matatar Dangote.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.