An Kaure a Majalisar Tarayya kan Rigimar Sarauta da Aka Bukaci Tinubu Ya Tsoma Baki

An Kaure a Majalisar Tarayya kan Rigimar Sarauta da Aka Bukaci Tinubu Ya Tsoma Baki

  • Yan Majalisar Tarayya sun kaure kan rigimar sarauta a yankin Okpella da ke karamar hukumar Etsako a jihar Edo
  • Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar yankin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta shiga lamarin domin dakile rasa rayuka
  • Sai dai ya zargi Mai girma Gwamna Godwin Obaseki kan lamarin bayan faduwa zaɓe inda ya fusata yan PDP a Majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An shiga rudani a Majalisar Tarayya da ke birnin Abuja kan rigimar masarauta a jihar Edo.

Majalisar ta ki amincewa da kawo kudiri da ke buƙatar Gwamnatin Tarayya ta tsoma a lamarin.

Rigima ta barke a Majalisar Tarayya kan matsalar nadin sarauta
Wasu yan Majalisar Tarayya sun kaure kan rigimar sarauta a jihar Edo. House of Representatives, Nigeria.
Asali: Facebook

An kalubalanci kudirin rigimar sarauta a Majalisa

Kara karanta wannan

Ambaliya ta tafka barna a wata jihar Arewa, gidaje 80 sun dulmiye a cikin ruwa

Punch ta ce dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Etsako ta Gabas da Yamma, Dekeri Anamero shi ya kawo kudirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai dan Majalisar ya ci karo da matsala inda mamba daga jihar Rivers, Awaji-Inombek Abiante ya kalubalance shi.

Tun farko, Dekeri Anamero ya bukaci tsoma bakin Gwamnatin Tarayya kan rigimar sarauta a kauyen Okpella da ke karamar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo.

Musabbabin abin da fusata yan Majalisar PDP

Anamero ya koka kan rasa rayuka sanadin nadin Lukman Akemokue da Gwamna Godwin Obaseki ya yi da al'umma suka bijire.

Ya ce gwamnan ya kakaba musu basaraken duk da korafin al'umma kan nadin sarautar inda suka nuna ba su so.

Har ila yau, Anamero ya zargi Obaseki da daukar matakin saboda faduwa zaben gwamna da PDP ta yi

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure tsakanin gwamnan jihar da 'yan kwadago, bayanai sun fito

Wannan kalamai na zargin faduwa zaɓe ne ya fusata dan Majalisar PDP daga jihar Rivers inda ya kalubalance shi.

An barke da rigima kan nadin sarauta

Mun ba ku labarin cewa zanga-zanga ta barke yayin da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya tabbatar da nadin sabon sarki.

Dattawa da shugabannin yankin Okpella a karamar hukumar Etsako sun yi fatali na nadin Lukman Akemokhue a matsayin sabon sarki.

Gwamna Obaseki ya tabbatar da nadin tare da mika takardar mukamin sarauta a ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.