Tuban Muzuru: Tubabbun Boko Haram Sun Tsere da Makamai, Suna Barazanar Kai Hari

Tuban Muzuru: Tubabbun Boko Haram Sun Tsere da Makamai, Suna Barazanar Kai Hari

  • Rahotanni na nuna wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram da suka tuba sun tsere da makaman da aka ba su domin yaki
  • Wasu daga cikin yan ta'addar sun fara barazanar kai munanan hare hare a jihar Borno bayan sun gudu sun koma cikin jeji
  • Wani masani a harkokin tsaro da ta'addanci ya yi ƙarin haske kan dalilan da suke saka yan ta'addar da suka tuba komawa ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rahotanni da suka fito daga Borno na nuni da cewa wasu daga cikin mayakan Boko Haram da suka tuba sun tsere.

An ruwaito cewa mayankan sun tsere da makaman da aka ba su domin taya sojojin Najeriya yaki da yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Yaki zai canza: An dauko salon hana yan bindiga yawo a jihohin Arewa

Borno
Yan Boko Haram da suka tuba sun gudu. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ce ta wallafa cewa wani mai fashin baki ya yi bayani kan dalilan da suke sanya tubabbun yan ta'addar guduwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake aiki da tubabbun Boko Haram

Gwamnati ta ware shiri na musamman na karbar yan Boko Haram da suka tuba domin killace su da koya musu sana'o'i.

Idan aka yi musu horo, ana daukar su domin su rika nunawa sojoji lungunan da sauran yan ta'addar suke.

Tsofaffin yan Boko Haram sun tsere da makamai

Daga cikin 'yan Boko Haram da aka daukan domin nunawa sojoji wurare, 13 sun tsere da makamai da babura.

Miyagun sun koma cikin jeji kuma an ruwaito cewa sun fara yin barazanar kai munanan hare hare kan al'ummar Borno.

Legit ta ruwaito cewa yan ta'addar sun yi wani bidiyo suna nunawa duniya makaman da suka tsere da su.

Kara karanta wannan

Basarake ya rasa ransa da Boko Haram suka shammaci motar sojoji, an rasa rayuka

Meyasa tubabbun Boko Haram ke guduwa?

Wani masanin harkokin tsaro da ta'addanci, Malik Samuel ya bayyana cewa yawanci ana yi musu alkawuran samun rayuwa mai dadi idan suka tuba amma hakan bai cika samuwa ba.

Malik Samuel ya kara da cewa akwai lokacin da tubabbun yan Boko Haram suka taba yin zanga zanga a sansanin da ake horar da su.

Gwamnatin tarayya ta kara shiri kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana nasarorin da rundunar sojin Najeriya ke cigaba da samu kan yan bindiga.

Bello Matawalle ya bayyana cewa suna shirye shiryen fito da wasu dabarun hana miyagu yan bindiga sakat musamman a Arewa ta Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng