Biyan Bashi da Mai: Dangote Ya ba Tinubu Shawarar Farfado da Matatun Najeriya

Biyan Bashi da Mai: Dangote Ya ba Tinubu Shawarar Farfado da Matatun Najeriya

  • Alhaji Aliko Dangote ya bukaci gwamnatin tarayya da ta daina amfani da danyen man da ake hakowa domin karbo lamunin kudi
  • Dangote ya ce jinginar da danyen mai tun kafin a hako shi na jawo karancin mai ga matatun kasar wanda ya kamata a kauce masa
  • Attajirin dan kasuwar ya kuma bayyana cewa akwai bukatar fadada samar da danyen mai domin biyan bukatun matatun man kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Alhaji Aliko Dangote, ya ce akwai bukatar Najeriya ta daina jinginar da danyen mai domin tabbatar da samuwar man ga matatun cikin gida.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya yi magana ne a wajen taron kungiyar masu matatun mai ta Najeriya da aka shirya a Legas.

Kara karanta wannan

Masu zuba jari a kasar Koriya za su gina matatun mai a Najeriya, bayanai sun fito

Dangote ya yi magana kan hanyar farfado da matatun man Najeriya
Dangote ya nemi gwamnatin tarayya ta daina jinginar da mai domin karbar bashi. Hoto: Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

"Gwamanti ta daina jinginar da mai" - Dangote

Jaridar The Punch ta ce Dangote ya nuna takaici kan yadda Najeriya ke amfani da danyen man da ko hakoshi ba a yi ba wajen karba da biyan basussuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Don tabbatar da cewa matatun cikin gida sun samu wadataccen danyen mai, akwai bukatar a dakatar da jinginar da danyen mai.
"Abin takaici ne a ce kasashe kamar Notways suna alkinta danyen man da za su hako wajen tara dukiya don amfanin gaba amma a ce Najeriya na salwantar da manta tun ba ta hako ba."

- A cewar Dangote.

Ta ya gwamnati ke jinginar da mai?

A ranar 4 ga Oktoba, 2024, jaridar Punch ta rahoto cewa, kamfanin NNPCL zai rika jinginar da ganga 272,500 na danyen mai a kowace rana a kan lamunin dala biliyan 8.86.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa har yanzu Dangote bai fara sayar da fetur kai tsaye ga ƴan kasuwa ba

Rahoton ya nuna cewa jinginar da ganga 272,500 na nufin cewa NNPCL zai biya basussuka daban daban da kusan ganga miliyan 8.17 na danyen mai a duk wata.

Dangote ya ba gwamnati shawara

Tribune ta rahoto Dangote, wanda ya samu wakilcin daraktan kamfanin, Mansur Ahmed, ya ce dole ne kasar nan ta ba da fifiko wajen amfani da danyen mai a cikin gida.

“Muna da bukatar ba da fifiko wajen aiwatar da aikin samar da danyen mai a cikin gida. Za mu buƙaci fadada ƙarfin samar da danyen mai domin cimma buƙatu daga matatunmu."

- A cewar Dangote.

Dangote ya bayyana cewa, akwai yiwuwar rufe wasu matatun mai a Turai da China, wadanda ke da karfin tace ganga miliyan 3.6 a kowace rana don haka dole gwamnati ta dauki mataki.

Dangote kadai zai samar da man jirgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ayyana Dangote a matsayin wadda zai rika samar da man jiragen sama ko Jet A1 ga kamfanonin jiragen Najeriya.

Kara karanta wannan

Dangote: Gwamnati ta fadi matata 1 da ta amince ta rika samar da man jiragen sama

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan, ya ce gwamnati ta yanke hukuncin ne bisa yardar kungiyar kamfanonin jiragen saman kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.