Wike vs Fubara: Mutane 4 da Za Su Iya Kawo Karshen Rikicin Siyasar Jihar Ribas

Wike vs Fubara: Mutane 4 da Za Su Iya Kawo Karshen Rikicin Siyasar Jihar Ribas

  • Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Ribas na 2023, Tonye Cole, ya koka da yadda ake ci gaba da rigingimun siyasa a jihar
  • Cole ya roki tsofaffin gwamnonin jihar uku da su zauna a teburin sansanci tare da ajiye bambancin siyasa domin dawo da zaman lafiya
  • A cewar shi, mutane hudu da za su iya shawo kan rikicin su ne Peter Odili, Rotimi Amaechi, Nyesom Wike da Gwamna Simi Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Dan takarar gwamnan Ribas a zaben 2023 karkashin jam'iyyar APC, Tonye Cole ya yi magana kan rikicin siyasar da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar.

Kara karanta wannan

Atiku ko Wike? Shugabanni sun bayyana wanda ya haddasa rikicin da ya mamaye PDP

Tonye Cole ya yi kira da a yi zaman sulhu tsakanin tsofaffin gwamnoni jihar, Peter Odili, Rotimi Amaechi, da Nyesom Wike da kuma gwamna mai ci Siminalayi Fubara.

Jigon PDP, Tony Cole ya roki mutane hudu da su kawo karshen rikicin Ribas
Tony Cole ya lissafa mutane hudu da za su iya kawo karshen tashe tashen hankula a Ribas. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Facebook

Jigon APC ya koka da rikicin Ribas

A tattaunawarsa da tashar Arise TV, jigon na APC ya yi imanin rigingimun da suka yi kaka-gida a tsakanin 'yan siyasar hudu ne tushen tashe-tashen hankula a Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ma damar aka ci gaba da tafiya a haka ba tare da an yi sasanci ba, to jihar za ta ci gaba da samun tashe-tashen hankula da ba a san ranar karewarsu ba.

Cole ya nuna rashin jin dadinsa da yadda aka mayar da rikicin siyasa ya zama al’adar Ribas, inda ya ce idan ba a samu sauyi ba, jihar za ta ci gaba da samun tashe-tashen hankula.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya bayyana dalilin barkewar rikici a jihar Rivers

Mutane 4 da za su hana rikicin Ribas

Maganganun 'dan takaran na jam’iyyar APC, sun yi daidai da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan a Ribas, wanda yake ganin dole ne a kawo karshensu.

"Wannan zaben kananan hukumomi ne, an cika shi da tashe tashen hankula, kuma a haka muke sa ran zaman lafiya? Hakan ba za ta yiwu ba.
"Dole ne Peter Odili, Rotimi Amaechi, da Nyesom Wike da kuma Gwamna Siminalayi Fubara su zauna a teburin sasanci, su ajiye bambancin siyasa gefe, a rungumi zaman lafiya."

- A cewar Tonye Cole.

PDP ta sake rikicewa kan Wike da Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa rigima ta kaure a wani taro da PDP ta gudanar a Abuja, inda bangarori biyu suka rika nuna juna da yatsa kan rikice-rikicen jam'iyyar.

A yayin da bangare daya ke ikirarin cewa Atiku Abubakar ne ya jawo rikicin jam'iyyar da ya ki ci ya ki cinyewa, dayan bangaren kuma sun ce Nysom Wike ne ya hargitsa PDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.