EFCC Ta Shiga Matsala da Gwamnoni 16 Suka Maka Ta a Kotu, An Samu Bayanai

EFCC Ta Shiga Matsala da Gwamnoni 16 Suka Maka Ta a Kotu, An Samu Bayanai

  • Gwamnonin jihohi 16 a Najeriya sun maka hukumar yaki da cin hanci ta EFCC a gaban Kotun Koli da ke birnin Tarayya Abuja
  • Jihohin na kalubalantar dokar da ta samar da kuma kirkirar hukumar EFCC da wasu guda biyu game da ayyukansu
  • Gwamnatin jihar Kogi ce ta fara korafi kan lamarin kafin daga bisani jihohi 15 su mara mata baya da korafe-korafensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta saka ranar zama kan korafin gwamnonin jihohi 16 da suka shigar da hukumar EFCC a gabanta.

Kotun ta sanya 22 ga watan Oktoban 2024 a matsayin ranar zama tare da yin hukunci kan korafin gwamnonin.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin abubuwa 63 da Gwamnatin Tinubu ta cirewa harajin VAT

Gwamnoni 16 sun maka hukumar EFCC a kotu
Gwamnoni 16 sun shiga kotu da hukumar EFCC. Hoto: Supreme Court.
Asali: Twitter

An maka hukumar EFCC a kotun tarayya

Tribune ta ruwaito cewa gwamnonin 16 suna kalubalantar dokar da ta samar da hukumar EFCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin alkalai mai mutane bakwai karkashin jagorancin Mai Shari'a, Uwani Abba-Aji shi ya sanya ranar zama kan shari'ar.

Tun farko, gwamnatin Kogi ce ta fara shigar da korafin ta bakin kwamishinan shari'a a jihar.

Jihohin da suka shigar da korafi kan EFCC

Daga bisani, jihohin Nassarawa da Kebbi da Sokoto da Katsina suka goyi bayan gwamnatin Kogi kan korafin, The Guardian ta ruwaito.

Sauran sun hada da Niger da Plateau da Jigawa da Benue da Ondo da Edo da Oyo da Ogun da Enugu da Anambra da Cross River.

Jihohin sun dogara cewa duk wani hukunci na karkashin kundin tsarin mulki ne inda suka ce duk dokar da ta saba haka to ta zama na banza.

Kara karanta wannan

Babu daraja: shugaban karamar hukuma na matsala kan zargin garkuwa da kisan kai

Kananan hukumomi: Kotu ta yi hukunci kan shari'ar

A baya, kun ji cewa Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar da gwamnoni 36 na ƙasar nan kan ƙananan hukumomi.

Kotun Ƙolin ta hana gwamnoni 36 na ƙasar nan tsige zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi daga muƙamansu, inda ta ce hakan ya saɓawa doka.

Tun da farko, kotun ta yi hukuncin cewa gwamnatin tarayya ta riƙa ba ƙananan hukumomi kuɗinsu kai tsaye ba ta hannun gwamnoni ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.