Bayanai Sun Fito kan Ganawar Buhari da Gwamna Radda a Daura

Bayanai Sun Fito kan Ganawar Buhari da Gwamna Radda a Daura

  • Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa a Daura
  • Dikko Umaru Radda ya bayyana dalilin kai ziyarar ga shugaba Muhammadu Buhari kwanaki bayan dawowarsa daga kasar waje
  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shafe kwanaki da dama a kasar Birtaniya a wata ziyara ta musamman da ya kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamna Dikko Radda ya kai ziyarar ne gidan tsohon shugaban kasar da ke karamar hukumar Daura a Katsina.

Kara karanta wannan

'Za mu gama da su,' Bayan rokon Turji, gwamna ya tsaurara matakai kan yan bindiga

Gwamna Radda
Dikko Radda ya gana da Buhari. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta samo bayanai kan yadda ziyarar ta kasance ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dikko Radda ya ziyarci Buhari a Daura

Gwamnan jihar Katsina ya kai wata ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yayin ziyarar, gwamna Dikko Radda ya mika godiya ga shugaba Buhari kan yadda yake ba da gudunmawa wajen cigaban jihar Katsina.

Ziyarar ta haɗa da wasu jiga jigan yan kwamitin zartarwa na jihar Katsina da sakatare na musamman ga gwamna Radda, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji.

Dalilin da ya sa Radda ya ziyarci Buhari

Gwamna Radda ya ce daga cikin dalilan ziyarar akwai neman shawari daga tsohon shugaban kasar kan yadda za a bunƙasa jihar Katsina.

Dikko Radda ya ce hakan na cikin ƙoƙarin hada manufofin jihar Katsina a jiya da yau domin sanin inda za a dosa wajen kawo gyara.

Kara karanta wannan

Yunwa: Buhunan shinkafar Tinubu sun isa Katsina, an fara rabawa talakawa

A karshe gwamnatin Katsina ta bayyana cewa daga cikin dalilan ziyarar akwai maraba da tsohon shugaban kasar bayan ya dawo gida Najeriya daga kasar waje.

Za a dauki karin yan sa-kai a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, ya kai ziyarar ba-zata wajen da ake ba yan sa-kai horo domin dakile miyagu yan bindiga.

A yayin ziyarar, gwamna Dikko Umaru Radda ya kara amincewa da daukar yan sa-kai 500 domin cigaba da farautar miyagu a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng