Majalisar Musulunci Ta Fadi Kokarin Sanata, Ta Wanke Shi Daga Zargin Ta'addanci

Majalisar Musulunci Ta Fadi Kokarin Sanata, Ta Wanke Shi Daga Zargin Ta'addanci

  • Majalisar shari'ar addinin Musulunci a kasar nan ta ba Shehu Umar Buba kariya bayan an zarge shi da daukar nauyin ta'addanci
  • Ana zargin Sanatan mai wakiltar jihar Bauchi ta Kudu da daukar nauyin wani kasungurmin dan ta'adda zuwa aikin hajji
  • Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka hukumar tsaro ta DSS ta fara binciken zargin, kuma an mika bayanai ga shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar ya samu goyon bayan majalisar koli ta shari'ar musulunci kan zargin da ake yi masa.

A bayan nan aka samu rahoton da ke alakanta fitinannen dan ta'adda, Abubakar Idris da ake zargi da kai munanan hare-hare wasu jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Yan ta'adda sun ji wuta, sun shiga hannun yan sanda a Abuja

Bauchi
Majalisar musulunci ta wanke Sanata Shehu Buba Umar daga zargin ta'addanci Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa shugaban majalisar musulunci ta kasa, Abdurrasheed Hadiyatullah da mataimakinsa Bashir Aliyu Umar sun yi martani kan zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar musulunci ta nesanta Sanata da ta'addanci

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa majalisar shari'ar addinin musulunci ta nesanta Sanatan Bauchi, Shehu Umar daga zargin ta'addanci da aka yi masa.

Majalisar ta bayyana cewa kowa ya san Sanata Shehu Umar Buba wajen jajircewa kan tabbatar da an magance matsalolin da ke jawo rashin tsaro a fadin Najeriya.

"Ana yi wa Sanata Buba sharri:" Majalisar musulunci

Sanarwar da majalisar ta musulunci ta fitar ta ce zargin Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Umar Buba da ta'addanci kazafi ne kawai.

Majalisar na ganin wasu mutane na son amfani da damar wajen gogawa Sanatan kashin kaji da yi masa bi ta da kullin siyasa.

Kara karanta wannan

An zargi sanata da biyawa dan ta'adda kujerar hajji, DSS ta fara bincike

Yadda aka zargi Sanata da alaka da ta'addanci

A wani labarin kun ji cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fara binciken Sanata Shehu Umar Buba bisa zargin daukar nauyin ta'addanci.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano wani hadimin Sanatan ya biyawa kasurgurmin dan ta'adda, Abubakar Idris kudin aikin haji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.