Sheikh Daurawa: Abubuwa 5 da Ake So Ka Yiwa Mahaifinka bayan Ya Rasu
Kano - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tunatar da daukacin 'ya'ya nauyin da ya rataya a wuyansu yayin da mahaifinsu ya kwanta dama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fitaccen malamin addinin ya ce akwai abubuwa biyar da ake so mutum ya yi wa mahaifinsa idan ya rasu domin sama masa rahama a yayin da ya ke kwance a kabari.
A wani faifan bidiyo na malamin da wani Abdul Balarabe ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna cewa dukanin abubuwan biyar na da matukar muhimmanci ga mamaci.
Ga jerin abubuwa biyar da ake so 'ya'ya su yiwa mahaifinsu idan ya rasu:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Yawaita yi masa addu'a
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce abu na farko da ake so 'ya'ya su yiwa mahaifinsu bayan rasuwarsa shi ne addu'a.
Malamin ya ce ka da 'ya'ya su gushe suna yi wa mahaifinsu addu'a har karshen rayuwarsu domin ubangiji na iya yiwa mahaifin garafa saboda addu'arsu.
2. Sadakatul Jariya
Abu na biyar shi ne 'ya'ya su yi wata sadaka mai gudana (Sadakatul Jariya) da sunan mahaifin, domin ya ci gaba da samun ladar wannan sadakar har tashin kiyama.
Malamin ya ce ana iya gina masallaci, makaranta, ko dakin karatu da fatan Allah ya kai ladar ga mahaifin mutu.
3. Biya masa bashi
A game da biyan bashi, Sheikh Aminu Daurawa ya ce akwai bukatar gaggauta nemo wadanda mamaci ya karbi bashinsu domin a biyasu hakkokinsu.
Ya ce ana so 'ya'ya su tabbatar sun nemo duk wanda mahaifin ya zalunta, ko ya ci hakkinsa domin biyan wannan hakkin ko nema masa gafara.
Idan mahaifin ya bude gidan rawa, ko gidan karuwai ko ya bar wani abu na sabon Allah, ana so 'ya'ya su gaggauta kawar da wannan gidan domin ragewa mahaifin azaba a kabarinsa.
4. Sada zumunci ga abokansa
Sheikh Aminu Daurawa ya ce idan har mahaifin mutum na da abokai, to akwai bukatar 'ya'yansa su ci gaba da sada zumunci da su, domin abokan za su rika yiwa mahaifin addu'a.
Malamin ya ce 'ya'ya na da hakki na ziyartar 'yan uwan mahaifinsu wanda hakan zai sa a rika tunawa da mahaifin ana yi masa addu'a wadda ke da matukar amfani ga mamacin.
Haka zalika, malamin ya ce akwai bukatar 'ya'ya su kasance masu aikata abubuwan da al'umma za su rika yiwa iyayensu addu'a bayan mutuwarsu.
5. Ziyartar kabarin mahaifi
Abu na biyar kuma na karshe da ake so 'ya'ya su yiwa mahaifi bayan rasuwarsa shi ne ziyartar kabarinsa domin yi masa addu'a a kai a kai.
Malamin addinin ya ce 'ya'ya su ziyarci kabarin mahaifinsu, su yi masa sallama ta kansa tare da juyawa Gabas domin yi masa addu'ar neman gafara da rahamar ubangiji.
Duba bidiyon a kasa wanda @PendingUstaz ya wallafa a shafinsa na X:
Ladubban da ake bi wajen yin addu'a
A wani labarin, mun ruwaito cewa akwai ladubba da ake so Musulmi ya kiyaye su gabani da kuma bayan gabatar da addu'a domin Allah ya amsa masa cikin gaggawa.
Daga cikin ladubban akwai tsarkake niyya, fara addu'a da yabon ubangiji, sakankancewa yayin addu'a, nacewa da rokon Allah, yin addu'a a lokacin tsanani da yalwa da sai sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng