Ayyukan Ibada 5 da ka iya amfanan mamaci a Musulunci

Ayyukan Ibada 5 da ka iya amfanan mamaci a Musulunci

Akwai wani fahimta maras asali da wasu ke kudirtawa cewa idan Musulmi ya mutu, bai zai iya amfana da addu'o'in wasu ba.

Amma Hadisan Manzon Allah (SAW) sun bayyana cewa akwai wasu ayyukan da ka iya amfanin Musulmi har bayan mutuwarsa.

1. Sallar Jana'izar da ake yi masa

Daya daga cikin abubuwan da ke amfanan mamaci shine Sallar Jana'izar da ake masa. Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa : "Na ji Manzon Allah (SAW) yace: Idan Musulmi ya mutu kuma mutane 40 marasa shirka ga Allah suka tsaya akan gawarsa. Allah zai basu cetonsa." [Sunan Abu Dawud 3170]

2. Sadaqatul Jaariyan da ya gabatar lokacin rayuwarsa

Daga cikin abubuwa masu muhimmanci da zasu amfana mamaci Musulmi shine Sadaqatul Jaariya da ya gabatar lokacin da yake rayuwa.

Misalin Sadaqatul Jaariyan da Musulmi zai iya amfana da su sune ginin Masallaci, Makarantar addini, gidan marayu, rijiya ko burtsatsan ruwan sha ga mabukata, da sauran su.

Abdullah bin Abu Qatadah ya ruwaito cewa mahaifinsa yace: "Manzon Allah (SAW) yace Abu mafi kyawu da mutum zai barin ma kansa uku ne: Dan kirkin da ke yi masa addu'a, Sadaqatul Jaariya da ke gudana, da ilmin da ya amfanar da mutane da shi." [Sunan Ibn Majah, 1/242]

3. Sadaqah da addu'oin da yaran mamacin sukayi masa

Addu'o'in yaran da mutum ya bari a baya na isan masa saboda irin tarbiyyan da yayi musu na zama ilmi

Ummuna Aisha tace: Wani mutum ya fadawa Manzon Allah (SAW) "Mahaifiyata ta mutu, kuma ina tunanin da zata iya magana, da ta yi sadaqa, shin zan iya Sadaqa a madadinta?" Manzon Allah (SAW) yace "Na'am, yi sadaqa a madadinta." [Sahih al-Bukhari 2760]

4. Biyan basukan mamaci da Cika Alkawuran da mamacin yayi

Hadisin Abdullahi ibn Abbas yace: Wata mata daga kabilar Juhaina ta zo wajen Manzon Allah (SAW) kuma tace, "Mahaifiyata ta yi alwashin yin aikin Hajji , amma ta mutu kafin yi, shin zan iya yi a madadinta?" Manzon Allah (SAW) yace, Yi Hajji a madadinta, shin da akwai bashi akanta, zaka biya ko ba zaka biya ba? Saboda haka, bashin Allah yafi cancanta a biya." [Sahih Bukhari 1852]

5. Ilmin da azurta mutane da shi lokacin da yake rayuwa

Ummuna Aisha tace: Wani mutum ya fadawa Manzon Allah (SAW) "Mahaifiyata ta mutu, kuma ina tunanin da zata iya magana, da ta yi sadaqa, shin zan iya Sadaqa a madadinta?" Manzon Allah (SAW) yace "Na'am, yi sadaqa a madadinta." [Sahih al-Bukhari 2760]

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng