Ma'aikatan NAFDAC Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, Sun Bayyana Dalili

Ma'aikatan NAFDAC Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, Sun Bayyana Dalili

  • Ma’aikatan NAFDAC sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a kan batun karin girma da wasu batu da har yau ba a warware ba
  • Ma'aikatan da suka shiga yajin aikin suna karkashin kungiyar manyan ma’aikata na hukumomi da kamfanonin mallakar gwamnati
  • Kungiyar ta umurci dukkanin ma’aikatan da suke karkashinta da su janye ayyukansu har sai an biya bukatun da suka zayyana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ma'aikatan hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani kan matsalolinsu da aka gaza magancewa.

An ce ma'aikatan karkashin kungiyar manyan ma’aikata na hukumomi da kamfanonin mallakar gwamnati, da ke cikin kungiyar kwadago ta TUC ne suka shiga yajin aikin.

Kara karanta wannan

Sauye sauye a majalisar ministoci: Tinubu zai saki sunayen ministocin da zai kora

Ma'aikatan hukumar NAFDAC sun sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ta gani
Ma'aikatan NAPDAC sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani. Hoto: @NAFDAC
Asali: Twitter

Ma'aikatan NAFDAC sun shiga yajin aiki

Jaridar Punch ta rahoto cewa ma'aikatan sun tsunduma wannan yajin aikin ne saboda gwamnati ta gaza magance matsalolin karin girma da kuma walwalarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatan sun ce shiga yajin aikin ya zama wajibi la'akari da cewa tarurrukan da suka yi da mahukuntan NAFDAC bai haifar da wani da mai ido game da bukatunsu ba.

Fusatattun ma’aikatan sun bayyana cewa har yanzu ba a magance koke-kokensu ba, lamarin da ya sa suka tsuduma yajin aikin inji rahoton Channels.

Bukatun da ma'aikatan suka gabatar

A cikin wata sanarwa da Dakta Ejor Michael, sakataren TUC ya rabawa manema labarai game da sanarwar shiga yajin aikin, ya bayyana cewa:

"Wannan matakin ya biyo bayan gazawar hukumar NAFDAC na magance muhimman batutuwan da aka zayyana a cikin wannan sanarwa"

Sanarwar ta zayyana bukatun da suka hada da:

Kara karanta wannan

Gwamna zai bankado ma'aikatan bogi, an kafawa ma'aikata sharadin karbar albashi

  • Bitar jarabawar karin girma ta shekarar 2024
  • Nada daraktoci na hulda da jama'a da aiyuka na musamman
  • Daukar nauyin horar da ma'aikata a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas
  • Gyara abubuwan da ke kunshe a jarabawar karin girma
  • Bayyana makin APER/PER/KPI a kan lokaci
  • Duba sharuɗɗan cancanta domin zana jarawabar karin girma
  • Ƙirƙirar ofishin nazartar tunani da dabi'u daidai da sanarwar HOS
  • Biyan duk kuɗin biso, inshorar rai da alawus ɗin zuwa gida
  • Biyan bashin albashi ga ma'aikata daga 2022, da sauran bukatu.

NAFDAC ta kona jabun kayayyaki

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukuma NAFDAC ta kona jabun kayayyaki daga Arewa maso Yamma na kasar nan da suka tasamma miliyoyin Naira.

An ce cikin kayayyakin da ta kwace kuma ta kona akwai wadanda wa'adin amfaninsu ya kare, yayin da wasu kuma su ke da illa ga lafiyar mutum.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.