Yanzu-yanzu: Hukumar NAFDAC ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnati

Yanzu-yanzu: Hukumar NAFDAC ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnati

- Hukumar DAFDAC ta sanar da stundumawa yajin aikin kwanaki bakwai a matsayin gargadi ga gwamnati

- Hukumar ta bayyana rashin jin dadinta ga yadda gwamnati ta gagara biyan mambobinta wasu kudaden alawus

- Ta bayyana cewa, akwai ma'aikata da dama da suka share shekaru ba a biyasu kudin alawus na karin girma ba

Kungiyar Likitocin da Ma’aikatan Lafiya na Najeriya (MHWUN) na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai., The Cable ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun Ejor Michael, kakakin MHWUN, yajin aikin ya fara ne da sanyin safiyar Alhamis.

Ma’aikatan na neman a biya su bashin kudaden karin girma na shekarar 2018 da 2019.

Sun kuma bukaci a sake duba alawus din takamaimai na aiki da kuma ci gaba da biyan kudin sallama.

KU KARANTA: Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Yanzu-yanzu: Hukumar NAFDAC ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnati
Yanzu-yanzu: Hukumar NAFDAC ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnati Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

“Kungiyar tana neman a biya ta bashin kudaden karin girma na shekarar 2018 da 2019 da suka bibiyi mambobinsu (ma'aikatan NAFDAC).

"Babban abin damuwa shine, ma'aikatan da aka ara musu girma a 2020 nan bada jimawa ba (suma) zasu shiga jerin. Wannan bukatar ta dade don haka aka fara yajin aikin,” in ji sanarwar.

“Ba a sake duba alawus na Musamman da aka biya ma’aikatan NAFDAC ba tsawon shekaru 10 ko makamancin haka. Yawancin lokaci, kowane alawus yana karuwa daidai da karin albashi.

"Amma kash, wannan bai kasance ba game da alawus na Musamman na Aiki ba. Don haka kungiyar ke neman a sake duba wannan takamaiman alawus din Aikin daidai da na Mafi qarancin Kudade na yanzu.

“Kungiyar ta fusata da dakatar da alawus da ake biya ga wadanda suka yi ritaya duk da cewa wannan tallafin ya samu karbuwa daga Hukumar Gudanarwar NAFDAC kuma tana kunshe ne a kan Sharadin aiki na ma’aikatan NAFDAC.

"Shugabannin kungiyar suna neman a dawo da biyan wannan alawus din nan take ga wadanda suka cancanta.”

Sauran batutuwan da kungiyar ta gabatar sun hada da matsalar karancin albashin ma’aikata, rashin kyakkyawan yanayin aiki, karancin motocin ma’aikata don saukaka matsalolin sufuri, da biyan kudin tallafin Korona.

KU KARANTA: Hauhawar tattalin arziki ya karu zuwa 18.17%, ya jawo tashin kayan abinci

A wani labarin, Kungiyar Likitocin Kasa (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 1 ga Afrilu, 2021.

Shugaban NARD din, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, ya fadawa jaridar The Nation dakatarwar ta dogara ne da wasu kyawawan sakamako daga tattaunawar da aka yi da gwamnati.

Duk da haka ya ba gwamnati wa'adin makonni hudu don biyan bukatunsu da suka koka akai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel