Kotu Ta Hana EFCC Gudanar da Bincike a wasu Jihohi 10, Olukoyede Ya Yi Bayani

Kotu Ta Hana EFCC Gudanar da Bincike a wasu Jihohi 10, Olukoyede Ya Yi Bayani

  • Hukumar EFCC ta bayyana cewa yaki da rashawa da take yi a kasar nan ya samu koma baya ne sakamakon gaza bincike a wasu jihohi 10
  • Shugaban hukumar, Olanipekun Olukoyede ya ce takunkumin da kotu ta kakaba ya haramta masu gudanar da bincike a jihohin nan
  • Olanipekun Olukoyede ya kuma roki kotunan kasar nan da su duba batun yawan ba masu laifi takardar umarnin hana EFCC kama su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Olanipekun Olukoyede ya nuna cewa EFCC ta samu koma baya a ayyukanta.

Olanipekun Olukoyede ya ce EFCC ba za ta iya gudanar da bincike a wasu jihohi 10 na Najeriya ba, sakamakon takunkumin da kotu ta saka mata.

Kara karanta wannan

Neman Tazarce a 2027: Manyan 'yan siyasar Kano da ke goyon bayan Shugaba Tinubu

Shugaban EFCC ya yi magana kan matsalolin da suke fuskanta a yaki da rashawa
Shugaban EFCC ya ce kotu ta hana hukumar gudanar da bincike a wasu jihohi 10. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Hukumar EFCC ta yi taro da alkalai a Abuja

Shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana hakan ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin kamar yadda Channels TV ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olukoyede ya yi maganar ne a taron karawa juna sani ga alkalai (EFCC-NJI) karo na shida a dakin taro na cibiyar shari’a ta kasa da ke Abuja.

Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa taken taron “Hada kan masu ruwa da tsaki wajen yaki da cin hanci da rashawa” ya dace da abin da ake son cimmawa.

Kotu ta kakabawa EFCC takunkumi a jihohi

Duk da cewa Olukoyede bai bayyana jihohin da abin ya shafa ba, amma ya koka da yadda ayyukan EFCC ke ci gaba da samun cikas sakamakon takunkumin kotu da ya hana bincike.

A cewarsa, daga cikin kalubalen da ke fuskantar EFCC akwai yadda kotuna ke dage shari’o’in manya-manyan laifuffuka da hana hukumar kama masu laifi da sauransu.

Kara karanta wannan

An samu karin bayani kan yadda ICPC ta kwato N13bn da aka handame a wata 1

Ya ci gaba da cewa, akwai bukatar kotuna su daina yawan ba wadanda ake zargi takardar umarnin hana EFCC kama su a duk lokacin da ake son bincikarsu.

Yayin da yake amincewa da matsaloli daga banagren hukumar ta EFCC, Olukoyede ya ce hukumar ta dauki wasu matakai na gyara tsarin bincikenta kamar yadda doka ta tanada.

Kotu ta hana EFCC kama Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa kotu ta ba hukumar EFCC umarnin dakatarwa na kamawa, daurewa, bincika ko cin zarafin Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutane.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan jam'iyyar NNPP, Kwankwaso da wasunsu sun shigar da kara gabanta domin hana hukumar EFCC gudanar da bincike a kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.