An Cafke Matashin da Ya Sassara Dan Banga har Lahira, Ya Yi Masa Sata

An Cafke Matashin da Ya Sassara Dan Banga har Lahira, Ya Yi Masa Sata

  • Rundunar yan sandan Ogun ta cafke wani matashi mai suna Faisal Audu da ake zargi da kisan gillar wani dan banga
  • Bayan kisan dan bangar mai suna Saheed Awolesi, an ruwaito cewa Faisal Audu ya sace wasu kayayyakinsa ciki har da babur
  • Rundunar yan sandan jihar Ogun ta yi karin haske kan yadda ake zargin an kashe Saheed Awolesi a daren ranar Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke wani matashi mai shekaru 20 kan zargin kisan gilla.

Rundunar yan sanda ta zargi matashin mai suna Faisal Audu da laifin kashe wani dan banga da kuma sace masa kayayyaki.

Kara karanta wannan

Lantarki ta babbaka ɓarawo da aka dawo da wuta yana satar waya

Yan sanda
Yan sanda sun kama wanda ya kashe dan banda. Hoto: Legit Hausa
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Faisal Audu ya amince da laifin da yan sanda suke zarginsa da aikatawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajali: Yadda dan banga ya fita da dare

Kakakin yan sanda a jihar Ogun, Omolola Otudola ta bayyana cewa dan bangar ya fita farauta ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:00pm.

Tun bayan fitansa aka wayi gari bai dawo gida ba wanda hakan ya saka iyalansa fita domin bincike kan abin da ya faru da shi.

An kama wada ya sassara dan banga

Biyo bayan binciken yan sanda, an cafke wani matashi mai suna Faisal Audu bisa zargin yi wa dan bangar kisan gilla.

Bayan tsananta bincike, Faisal ya amince da aikata laifin kuma ya jagoranci yan sanda wajen da ya kashe dan bangar kuma an samo gawarsa a wajen.

Matashi ya yi sata ga dan banga

Kara karanta wannan

Yan sanda sun mutu bayan yan bindiga sun cilla musu bam, an dauki mataki mai tsauri

Yan sanda sun samu babur, arda, wayar hannu da jakar wuka mallakar dan bangar a hannun matashin da ake zargi da kisan.

A yanzu haka dai rundunar yan sanda ta ce ta kai gawar dan bangar asibiti a domin cigaba da bincike kan abin da ya faru.

An kashe wasu 'yan bindiga a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda sun tafka kazamin fada da yan bindigar da suka yi yunkurin sace matar dan majalisa a jihar Delta.

Rundunar yan sanda ta yi nasarar bude wuta ga yan bindigar kuma uku sun sheka lahira yayin da aka kai su asibiti bayan samun raunuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng