Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga a Kaduna, Sun Ceto Mutane 7 da Suka Sace

Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga a Kaduna, Sun Ceto Mutane 7 da Suka Sace

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai wani samame a maɓoyar ƴan bindiga da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna
  • Sojojin sun yi nasarar sheƙe ƴan bindiga uku tare da raunata wasu a sansanin da ke ƙauyen Kurmin-Kare a cikin ƙaramar hukumar
  • Jami'an tsaron sun kuma samu nasarar ceto wasu mutum bakwai da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su kamar yadda aka ji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sojoji sun bindige ƴan bindiga uku a wani samame a maɓoyarsu da ke jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun kuma ceto mutum bakwai daga hannun ƴan bindigan a maɓoyarsu da ke ƙauyen Kurmin-Kare cikin ƙaramar hukumar Kachia.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Kaduna
Sojoji sun sheke 'yan bindiga a Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun sace makiyaya uku da suka je sayar da shanunsu tare da wasu mata huɗu lokacin da suke dawowa daga kasuwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban makaranta da wasu mutum 8 a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka fatattaki ƴan bindiga

Wani ɗan banga wanda yana ɗaya cikin waɗanda suka jagoranci sojoji zuwa sansanin ƴan bindigan, ya ce an kai samamen ne da ƙarfe 4:12 na yammacin ranar Asabar.

Ƴan bayyana cewa ƴan bindigan sun gudu sun bar mutanen ne bayan jami'an tsaron sun buɗe musu wuta.

Wani shugaban al'umma a yankin ya tabbatar da ceto mutanen guda bakwai daga hannun ƴan bindigan.

"Eh da gaske ne sojoji kun kuɓutar da wasu Fulani ciki har da mata waɗanda ke dawowa daga kasuwar ƙauyen SCC da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su."

- Wani shugaba

Ya bayyana cewa tun da farko ƴan bindiga sun buƙaci a ba su N30m a matsayin kuɗin fansa, inda ya ƙara da cewa sun ƙwace kuɗi masu yawa a hannun Fulanin.

Me jami'an tsaro suka ce kan lamarin?

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban basarake da wasu mutane a Kebbi

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa a jira shi zai sake kiran wayarmu daga baya.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Kachia a daren ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban inda suka yi garkuwa da mutane.

Daga cikin mutanen da ƴan bindigan suka sace har da wani shugaban makarantar sakandiren gwamnati a garin. Ana maganar an sace mutane kusan 10.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng