Bayan Zama Gwamna na 1, Abba Gida Gida Ya Kara Samun Lambar Girmamawa

Bayan Zama Gwamna na 1, Abba Gida Gida Ya Kara Samun Lambar Girmamawa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara samun lambar girmamawa kan ayyukan da ya ke gudanarwa a Kano
  • Lambar yabon ta baya-bayan nan na zuwa bayan gwamnan ya zama gwarzo a cikin gwamnonin Najeriya
  • A wannan jikon, malamai ne su ka ga dacewar karrama gwamnan bisa kokarinsa na farfado da ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake samun lambar girmamawa kan muhimmin aikin da ya ke gudanarwa a jiharsa.

Wannan shi ne karo na biyu da gwamnan ke samun lambar girmamawa a kasa da mako guda saboda zarra da ya yi tsakanin takwarorinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi illar gobarar kasuwa ga Kano, Abba ya yi wa 'yan kasuwa alkawari

Abba Gida Gida
Malamai sun karrama gwamnan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da karbar lambar yabon da kungiyar malamai ta kasa (NUT) ta mika masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NUT ta ba gwamna Abba lambar girmamawa

Jaridar The Nation ta wallafa cewa kungiyar malamai ta kasa (NUT) hadin gwiwa da ma'aikatar ilimi ta Najeriya ta karrama gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Shugaban NUT, Kwamred Titus Ambe ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya cancanci karramawar tare da wasu gwamnoni biyar saboda aikin farfado da ilimi a jihohinsu.

Lambar girmamawa: Ayyukan gwamna Abba kan ilimi

Wasu daga cikin ayyukan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi har ya samu lambar yabo sun hada da sanya dokar ta baci kan bangaren ilimi a Kano.

Sannan gwamnatin jihar ta ware 29.9% na kasafin kudin bana ga bangaren ilimi domin ba ta damar gudanar da ayyukan raya fannin tun daga matakin farko a fadin Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya yabi Fubara kan bijirewa 'kutse' a zaben kananan hukumomin Ribas

Gwamna Abba ya samu lambar yabo

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zarra tsakanin sauran gwamnonin kasar nan 35 inda ya zama gwamna mafi kwazo.

Jaridar Africa Trust Magazine ce ta ga dacewar ba gwamnan lambar yabo kan zage damtsen gwamnatinsa wajen ayyukan ci gaban al'umma, kuma tuni mutanen Kano su ka fara sa albarka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.