Rai Ɓakon Duniya: Ministar Buhari Ta Tafka Babban Rashin Ɗanta 1 Tilo a Duniya

Rai Ɓakon Duniya: Ministar Buhari Ta Tafka Babban Rashin Ɗanta 1 Tilo a Duniya

  • Tsohuwar Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen ta tafka babban rashin ɗanta guda daya tilo
  • Marigayin mai suna Richard ya rasu ne a jiya Asabar 6 ga watan Oktoban 2024 a wani asibiti da ke Abuja
  • Mrs Tallen ta rike muƙamin Ministar mata a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Tsohowar Minista a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tafka babban rashi.

Mrs Pauline Tallen wacce ta rike muƙamin Ministar harkokin mata ta rasa ɗanta guda daya tilo.

Dan tsohuwar Minista 1 tilo a duniya ya kwanta dama
Tsohuwar Minista a mulkin Muhammadu Buhari, Pauline Tallen ta tafka babban rashi. Hoto: Pauline Tallen.
Asali: Twitter

Yaushe marigayin ya kwanta dama a Abuja?

Marigayin mai suna Richard mai shekaru 42 ya rasu ne a jiya Asabar 5 ga watan Oktoban 2024, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta tafka barna a wata jihar Arewa, gidaje 80 sun dulmiye a cikin ruwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar cewa an kwantar da marigayin a asibitin Cedar Crest da ke birnin Tarayya, Abuja.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu tabbacin musabbabin mutuwar dan tsohuwar Ministar ba.

Iyalai da 'ya'ya da marigayin ya bari

Kungiyar tsofaffin dalibai ta makarantar da Richard ya halarta mai suna VOBA ta sanar da haka a shafin Facebook inda ta marigayin ya rasu a Abuja bayan fama da jinya.

"Mu na mai bakin cikin sanar da ku rasuwar daya daga cikin mambobin wannan kungiya, Mr Richard Adamu Tallen."
"Marigayin ya rasu ne a jiya Asabar 5 ga watan Oktoban 2024 bayan ya sha fama da jinya a asibitin Abuja."

- Cewar sanarwar

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya bar duniya yana da mata da kuma ya'ya guda uku.

Kara karanta wannan

Shugaban Izala ya rasu, al'ummar Musulmi sun shiga jimami

Har ila yau, marigayin ya kammala karatun digiri dinsa a tsangayar kimiyyar na'ura mai ƙwaƙwalwa a Jami'ar Amurka.

Mahaifiyar tsohon gwamna ta rasu

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame ya tafka babban rashi bayan mutuwar mahaifiyarsa a jiya Asabar.

Marigayiyar, Mama Jummai Eli Nyame Kala ta rasu ne cikin salama a daren jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.

Sakataren yada labaran tsohon gwamnan, Hon. Obidah Bitrus shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.