Ministan harkokin mata, Pauline Tallen ta harbu da cutar korona
- Pauline Tallen, ministan harkokin mata ta kamu da muguwar cutar korona
- Ta tabbatar da hakan ne a wata wallafa da ta yi a ranar Asabar kuma ta saka hannu
- Ta sanar da cewa a gwajin da dukkan iyalanta suka yi, ita kadai ta tabbata da cutar
Ministan harkokin mata, Pauline Tallen ta kamu da cutar korona, Channels TV ta tabbatar da hakan.
An tabbatar da kamuwarta ta muguwar cutar bayan da ta yi gwaji tare da iyalanta.
Kamar yadda ta fitar da takardar da ta sa hannu a ranar Asabar, ministan ta ce har yanzu babu wata alamar cutar da ta fara bayyana a tare da ita amma an shawarceta da ta killace kanta.
KU KARANTA: Bill Gates: Har yanzu mun rasa dalilin da yasa Korona bata tsananta a Afrika ba
Amma kuma ta tabbatar da cewa babu wani a gidanta da ya kamu da cutar bayan ita.
Ta killace kanta inda take samu kulawar likitoci.
KU KARANTA: Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa
A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nuna yadda yake da burin kawo karshen kalubalen da ke addabar arewa ta tsakiya a fannin tsaro.
A wasu hotunansa, an ga gwamnan jihar Kogin sanye da kayan sojoji inda ya tsinkayi dajin Irepeni da ke Kogi ta tsakiya domin ganawa da sojojin da ke dajin.
Wani Promise Emmanuel wanda ya bayyana kansa a matsayin babban sakataren yada labaran mataimakin gwamnan ya wallafa hotunan a Twitter a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba.
Mataimakin gwamnan jihar Kogi ya sake wallafa hotunan a shafinsa na Twitter, Legit.ng ta gano hakan.
Promise wanda ya bayyana cewa ziyarar gwamnan ya yi ta ne a watan Maris na 2018, ya kara da cewa gwamnan ya je duba yadda ayyukan sojojin suke gudana ne a Irepeni.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng