Murna yayin da Gwamna Ya Sanar da Lokacin Fara Biyan Mafi Karancin Albashi
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ba ma'aikata tabbacin cewa zai fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000
- Gwamna Makinde ya bayyana cewa zai ci gaba da mayar da hankali wajen jindaɗin ma'aikatan jihar ta yadda za su ji daɗin gudanar da ayyukansu
- Ya bayyana hakan ne a wajen bikin ranar malamai ta duniya na shekarar 2024 wanda aka gudanar a ranar Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa zai fara biyan mafi ƙarancin albashin da zarar an daidaita batun ƙarin da za a yi a albashin.
Gwamna Makinde ya kuma sanar da ƙarawa ma’aikata albashin N25,000 da kuma ƙarin albashin N15,000 ga ƴan fansho na watanni uku, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Makinde zai biya ma'aikata N70,000
Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a yayin bikin ranar malamai ta duniya na shekarar 2024 wanda aka gudanar a daƙin taro na NUT a Apata cikin birnin Ibadan, babban birnin jihar, rahoton Vanguard ya tabbatar.
"A kan mafi ƙarancin albashi, za a fara tattaunawa a mako mai zuwa kuma za mu biya mafi ƙarancin albashin N70,000. Amma za mu tattauna kan ƙarin da za a yi. Tawagar mu da ta ƙungiyar NLC za su zauna domin tattaunawa a kai."
- Seyi Makinde
Gwamna Makinde ya yabawa malamai
Gwamna Makinde ya yabawa malaman jihar kan irin ɗimbin goyon bayan da suka ba shi a lokacin zaɓen da ya gabata da kuma gudunmawar da suke badawa wajen gina jihar.
Gwamna Makinde ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko kan jin daɗin malamai da ma’aikatan gwamnati a jihar ta yadda za su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Gwamna Soludo zai fara biyan N70,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya shirya biyan ma'aikata mafi karancin albashi na N70,000.
Gwamna Charles Soludo ya yi alƙawarin fara biyan sabon albashin a ƙarshen watan Oktoban shekarar 2024.
Asali: Legit.ng