Emefiele: EFCC Ta Mika Sabuwar Bukata Gaban Kotu kan Tsohon Gwamnan CBN

Emefiele: EFCC Ta Mika Sabuwar Bukata Gaban Kotu kan Tsohon Gwamnan CBN

  • Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa na son babbar kotun tarayyya da ke Legas ta ƙi amincewa da buƙatar Godwin Emefiele
  • Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya ya buƙaci kotun da ta hana ƙwace masa $2.045m da wasu kadarorinsa
  • Hukumar EFCC wacce aka ba iznin ƙwace kuɗaɗen da kadarorin ta ce tsohon gwamnan na CBN bai ɗaukaka ƙara kan hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta buƙaci babbar kotun tarayya da ke zama a Legas ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Godwin Emefiele dai ya buƙaci kotun da ta dakatar da umarnin ƙwace wasu kadarori da kudaɗensa.

Kara karanta wannan

Wata ƙungiyar addinin Musulunci ta dura kan Shugaba Tinubu, ta faɗa masa gaskiya

EFCC ta bukaci kotu ta yi watsi da bukatar Emefiele
EFCC na son kotu ta ki amincewa da bukatar Emefiele Hoto: @OfficialEFCC, @cenbank
Asali: Twitter

A ranar 25 ga watan Agusta, 2024, kotu ta ba EFCC izinin karɓe kuɗaɗen da suka kai $2.045m na wani ɗan lokaci, da wasu kadarori guda bakwai, da kuma hannayen jarin da ke da alaƙa da Emefiele, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace buƙata Emefiele ya nema?

Leadership ta ce a ci gaba da shari’ar a ranar Juma’a, Lauyan Emefiele, Olalekan Ojo, ya buƙaci mai shari’a Deinde Dipeolu da ya dakatar da ci gaba da shari’ar har sai an yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da tsohon gwamnan na CBN ya shigar.

"Muna kira ga mai girma mai shari'a da ya dakata har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukuncin kotun ɗaukaka kara domin gujewa cin mutuncin shari'a."

- Olalekan Ojo

EFCC ta miƙa buƙata gaban kotu

Sai dai lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya ƙi amincewa da buƙatar. Ya bayyana cewa tsohon gwamnan na CBN bai ɗaukaka wata ƙara ba.

Kara karanta wannan

"PDP ta mutu," Kwankwaso ya bayyana jam'iyyar da ta yunƙuro da ƙarfinta a Najeriya

Mai shari'a Deinde Dipeolu ya ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har zuwa ranar 11 ga watan Oktoba domin yin hukunci kan wannan buƙatar.

EFCC ta gurfanar da tsohon gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a babbar kotun Abuja kan tuhumar zamba.

EFCC ta gurfanar da Ishaku tare da tsohon babban sakataren ma'aikatar kananan hukumomi da sha'anin masarautu a Taraba, Bello Yero gaban mai shari'a Sylvanus Oriji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng