An Samu Asarar Rayuka bayan 'Yan Bindiga Sun Yiwa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hare-haren kwanton ɓauna kan jami'an tsaro a ƙananan hukumomi biyu na jihar Katsina
- Ƴan bindigan a yayin hare-haren da suka kai sun hallaka jami'an rundunar KSWC mutum huɗu da ƴan banga mutum biyar
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nuna alhininsa kan wannan mummunan harin da ƴan bindigan suka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare kan jami'an tsaro a jihar Katsina
Hare-haren da ƴan bindigan suka kai a yammacin ranar Juma’a ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro mutum tara.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kuma sace manyan bindigogi guda shida a yayin harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
A cewar wata majiya, harin na farko ya faru ne a lokacin da wasu gungun ƴan bindiga ɗauke da manyan muggan makamai suka yiwa jami'an tsaro na rundunar KSWC da ƴan banga kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Faskari.
Ƴan bindigan sun yi musu kwanton ɓaunar ne lokacin da suke aikin ba da tsaro ga manoman da suke girbin amfanin gona a Unguwar Kafa da ke kan hanyar titin Yankara zuwa Faskari.
A yayin harin ƴan bindigan sun hallaka jami'an rundunar KSWC mutum huɗu da ƴan banga mutum biyu.
A wani harin na daban da aka kai a yammacin ranar, wasu gungun ƴan bindiga sun yiwa ƴan banga daga ƙaramar hukumar Matazu da ke kan hanyar Gwarjo zuwa Yalwa kwanton ɓauna.
A yayin harin, ƴan bindigan sun kashe ƴan banga uku, sannan mutum ɗaya ya samu munanan raunuka.
Gwamna Radda ya yi alhini
Jaridae Vanguard ta ce bayan hare-haren, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya jajantawa iyalan jami'an tsaro da suka rasu. Ya yaba da jajircewarsu da sadaukarwar da suka yi wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ba da dukkanin gudunmawar da ta dace ga iyalan mamatan.
Ƴan bindiga sun kashe jami'in tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga masu garkuwa da mutane sun kashe wani jagoran yan banga mai suna Lukman Bologun a Kwara.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe jagoran yan bangar ne bayan ya fafata da yan bindiga a wani fada da suka yi.
Asali: Legit.ng