Rivers: Zanga Zanga Ta Barke ana Tsaka da Gudanar da Zabe, an Gano Dalili

Rivers: Zanga Zanga Ta Barke ana Tsaka da Gudanar da Zabe, an Gano Dalili

  • Magoya bayan ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike sun fito kan tituna domin nuna adawarsu da zaɓen ƙananan hukumomin da ake yi a jihar Rivers
  • Masu zanga-zangar sun buƙaci Gwamna Siminalayi Fubara da ya bi umarnin kotu wanda ya hana a gudanar da zaɓen a jihar
  • Zanga-zangar na zuwa ne yayin da mutane suka fito domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na ranar Asabar mai cike da cece-kuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Ɗaruruwan magoya bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun gudanar da zanga-zanga a jihar Rivers.

Magoya bayan na Wike waɗanda ƴan jam'iyyar PDP ne sun fito zanga-zangar ne domin nuna adawa da zaɓen ƙananan hukumomin da ake yi a jihar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kutsa daji sun sheke babban ɗan bindiga, sun ceto wani Sarki

Zanga zanga ta barke a Rivers
Zanga zangar adawa da zabe ta barke a Rivers Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A yau ne dai ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar duk da umarnin da kotu ta ba da na hana gudanar da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa suka fito zanga-zangar?

Masu zanga-zangar sun bazama kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da matakin da Gwamna Siminialayi Fubara ya ɗauka na ci gaba da gudanar da zaɓen, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Mutanen dai sun fara hallara ne a gidan Polo da ke Yenagoa kafin su fara zanga-zangar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Sun fara tattakin ne a babban titin Aba da ke Port-Harcourt ɗauke da tutoci da kwalaye da rubuce-rubucen da ke kira ga Fubara da ya yi biyayya ga hukuncin babbar kotun tarayya wanda ya soke zaɓen.

An kuma tattaro cewa ɗaruruwan ƴaƴan jam’iyyar APC ne ke taruwa a sakatariyar jam’iyyar da ke Port- Harcourt domin gudanar da irin wannan zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Matawalle: Kungiya ta fito ta nemi afuwar ministan Tinubu

Abin fashewa ya tashi a sakatariyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ƴan daba ne, sun tayar da bama-bamai a sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Rivers.

Waɗanda ake zargin dai sun tayar da ababen fashewar ne da sanyin safiyar ranar Asabar a sakatariyar da ke birnin Port-Harcourt, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng