Wike Ya ba 'Ya 'yan Buhari, Manyan Yan Siyasa Wa'adin Mako 2 kan Filayensu a Abuja

Wike Ya ba 'Ya 'yan Buhari, Manyan Yan Siyasa Wa'adin Mako 2 kan Filayensu a Abuja

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba 'ya'yan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da wasu yan siyasa wa'adin mako biyu
  • Wike ya ba da wa'adin ne domin biyan kudin da ake binsu na filaye a yankin Maitama II saboda samun satifiket na mallakarsu
  • Hukumar FCTA a birnin ita ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta yi barazanar kwace su idan ba a bi ka'idar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar (FCTA) a birnin Abuja ta ba wasu manyan Najeriya wa'adin makwanni biyu ko ta kwace filayensu.

Hukumar ta ba 'ya'yan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da wasu manyan yan siyasa wa'ad kan rashin biyan sauran bashin da ake binsu.

Kara karanta wannan

"Na ji zafi sosai" Buhari ya magantu kan iftila'in da ya faru a Niger, ya kora ruwan addu'o'i

Wike ya yi barazanar kwace filayen 'ya'yan Buhari da wasu yan siyasa
Nyesom Wike ya yi barazana ga 'ya'yan Muhammadu Buhari da wasu yan siyasa kan filayensu a Abuja. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Wike ya ba yan siyasa wa'adi kan filaye

Premium Times ta ruwaito cewa daga cikinsu akwai shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila da sanatoci da tsofaffin gwamnoni da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada tsohon shugaban Majalisar Tarayya, Bukola Saraki da kakakin Majalisa, Abbas Tajudden da wasu Ministocin Bola Tinubu.

Har ila yau, akwai tsofaffin Ministoci a gwamnatin Muhammadu Buhari da 'ya'yansa, Yusuf da kuma Zahra Buhari.

"Dukan wadanda abin ya shafa su biya kudaden da ake binsu da na haya da sauran kudaden da ya shafi filayen kafin wa'adin da aka bayar ya kare."
"Rashin bin ka'idar da aka gindaya zai iya sanya Ministan Abuja, Nyesom Wike kwace filayen daga gare su."

- Cewar sanarwar

Gargadin da Wike ya yiwa yan siyasa

Hukumar ta ba da wa'adin ne game da filayen da ke yankin Maitama II a Abuja saboda karisa biyan kudi da karbar satifiket.

Kara karanta wannan

“An samu tsaro a Najeriya”: Ribadu ya fadi bambancin gwamnatin Tinubu da Buhari

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke shirin gudanar da manyan ayyuka a yankin da ke birnin.

Wike ya yi sanadin ba da mukamin Minista

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake samun yabo na musamman a wurin karamin Ministan man fetur, Heineken Lokpobiri.

Lokpobiri ya bayyana yadda Wike ya taka rawa ta musamman wurin tabbatar da ganin ya samun muƙamin Minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Ministan ya bayyana wasu muƙamai da tsohon gwamnan Rivers, Wike ya yi sanadi musamman a wannan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.