'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Ɗan Siyasa da Wani Shugaban Al'umma a Najeriya
- Ƴan bindiga sun kai farmaki ana tsaka da ruwan sama, sun yi awon gaba da wani jigon APGA da shugaban al'umma a Anambra
- Ganau sun bayyana cewa sun jiyo karar harbe-harben bindiga da safiyar ranar Jumu'a amma ba wanda ya fito saboda ruwan sama
- Rundunar ƴan sanda reshen Anambra ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce tuni ta fara ɗaukar matakan da suka dace don ceto su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ƙungiyar ci gaban Umunze da ke ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, Ezekiel Iheazor a jihar Anambra.
Maharan sun yi awon gaba da nutumin tare da wani jigon jam'iyyar APGA, Nze Ike Okoli a Anambra, ɗaya daga cikin jihohin Kudu maso Gabas.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a gidan Okoli da ke kauyen Lomu a lokacin da ake ruwan sama, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindigar suka sace mutum 2
Ganau sun shaida cewa ƴan bindigar sun buɗe wuta domin tsoratar da mutane, kana daga bisani suka kutsa cikin gidan da sanyin safiyar ranar Juma'a.
A cewar waɗanda abin ya faru a idonsu, maharan sun tasa nutanen biyu zuwa cikin motar da suka zo da ita, kana suka yi awon gaba da su.
Wata majiya ta ce:
"Eh gaskiya ne, an yi garkuwa da shugabanmu (PG) da wani mutum guda yau a Nkwo, ranar da babbar kasuwa ke ci, ga shi an tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.
"Mun ji karar harbe-harbe amma babu wanda ya fito saboda ruwan sama. Bayan da ruwan ya lafa, sai muka tuntubi abokanmu a kasuwar suka ce mana ba abin da ya faru.
"Jim kaɗan bayan haka wani shugabanmu ya faɗa mana abin da ya faru, da muka je wurin mun ga motar Iheazor a gidan Okoli, har yanzu dai ba a ji daga masu garkuwan ba."
Ƴan sanda suka fara ɗaukar matakai
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin lokacin da aka tuntubi shi ta wayar tarho.
“Rundunar ‘yan sanda ta samu labarin kuma ta fara ɗaukar matakai da neman ƙarin bayanin da zai taimaka wajen ceto mutanen," in ji Ikenga.
Anambra: An kashe ƴan sanda 2
A wani rahoton kuma wasu yan bindiga sun hallaka jami'an yan sanda a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Lamarin dai ya faru ne da safiyar ranar Alhamis da ta gabata, 3 ga watan Oktoban 2024 a Uruagu da ke karamar hukumar Nnewi.
Asali: Legit.ng