Gwamnan Bauchi Ya Karbe Masu Filin Idi, Sheikh Dutsen Tanshi Ya Fadi Abin da Zai Yi

Gwamnan Bauchi Ya Karbe Masu Filin Idi, Sheikh Dutsen Tanshi Ya Fadi Abin da Zai Yi

  • Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya koka game da yadda aka yanka filin da shi da mabiyansa su ke yin sallar idi
  • A martanin da ya yi, ya zargi gwamna Bala Mohammed da taba malamin addinin duk da wa’azin da aka yi masa
  • Dr. Dutsen Tanshi ya bayyana matakin da za su dauka tare da tunawa gwamnan lokacin da ya rage masa a ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Da alama sabanin Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi da Mai girma gwamna Bala Mohammad bai kare ba a jihar Bauchi.

An ji Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya na zargin gwamnatin Bala Mohammed da yanka filin da shi da mutanensa su ke sallar idi.

Dutsen Tanshi Majlis Bauchi
Dr. Dutsen Tanshi Majlis Bauchi ya ce Gwamnan Bauchi ya yanka filin idinsu Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi
Asali: Facebook

An ji shehin ya na maganar ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Masoyin Imam Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi a Facebook.

Kara karanta wannan

"Na ji zafi sosai" Buhari ya magantu kan iftila'in da ya faru a Niger, ya kora ruwan addu'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin musuluncin yake cewa wasu sun kira shi a wayar salula, wasu kuma sun same shi domin ankarar da shi abin da ya faru.

Gwamnan Bauchi ya yanka filin idi?

Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi ya ce gwamnati ta yanka wurin da suke sallar idi an rabawa mutane kuma sun fara yin gine-gine.

Saboda haka ya aika aka je aka bincika kuma zargin ya tabbata, malamin ya ce shi ma ya bi ta hanyar kuma ya ganewa idanunsa.

"Abin da zan fada ba za wuce kalmomi biyu ko uku ba idan sun yi nauyi.
"Abin da Abdul Mutallib (kakan Manzon Allah SAW) ya fadawa Abrahata lokacin da ya zo zai rushe dakin ka’aba.
"Sai ya ce a je a fada masa; dakin nan da Mai shi, idan Ya ga dama ya bar sa, idan ya ga dama Ya kama shi.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

- Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ga gwamnan Bauchi

Malamin ya fadawa gwamnan jihar Bauchi cewa akwai mai kasa kuma Allah SWT ya na da ikon damkarsa ko kuwa ya kyale shi.

Dr. Dutsen Tanshi wanda ya bar Bauchi kwanaki ya kawo misali da yadda Abba Kabir Yusuf ya rusa shagunan filin idi a Kano.

A bayaninsa, malamin ya tunawa gwamna Bala Mohammed cewa shekaru biyu da ‘yan watanni suka rage a cikin wa’adinsa a mulki.

Wani mataki Dutsen Tanshi zai dauka?

Malamin ya ce idan yau kai ne, gobe ba kai ba ne, ya na mai zargin gwamnan Bauchi da taba addini, akasin sauran gwamnonin Arewa.

Dutsen Tanshi da mabiyansa sun ce ba za su rushe ginin da aka yi ba, amma su na fatan Allah SWT ya kawo gwamnatin da za ta rusa.

Sheikh Dutsen Tanshi ya ba Tinubu shawara

Kara karanta wannan

"Na shirya rantsewa da Alƙur'ani ban taɓa satar ko kwabo ba," Tsohon gwamna El Rufai

Kwanakin baya aka rahoto cewa Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya ce idan Bola Tinubu ya na so a zauna lafiya sai ya maido tallafin fetur,

Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya soki tsarin da gwamnan CBN ya bi na sakin farashin Naira a kasuwa, ya ce an dauko fadan da babu riba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng