‘Ya Lalata Komai,’ Kwankwaso Ya Tono ‘Barnar’ da Ganduje Ya yi a Kano

‘Ya Lalata Komai,’ Kwankwaso Ya Tono ‘Barnar’ da Ganduje Ya yi a Kano

  • Tsohon gwamna Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi hira da manema labarai kan harkar ilimi a jiya da yau a jihar Kano
  • Sanata Rabi'u Kwankwaso ya zargi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da lalata harkokin ilimi a jihar a shekaru takwas
  • Haka zalika jagoran NNPP ya yabawa Abba Kabir Yusuf kan yadda ya dauko shirin farfoda da ilimi a dukkan kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi magana kan yadda ilimi ya kasance a karkashin mulkin Abdullahi Ganduje.

Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce bayan dawowa mulki sun samu lamura sun lalace ba kamar yadda suka barsu ba.

Kara karanta wannan

'Yan APC maƙiya talaka ne,' Kwankwaso ya kawo mafita da ya illata jam'iyyar

Kwankwaso|Ganduje
Kwankwaso ya zargi Ganduje da lalata ilimi. Rabi'u Musa Kwankwaso|Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Hadimin Rabi'u Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya wallafar bidiyon hirar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Kwankwaso ya gyara ilimi a Kano

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana cewa ya gyara makarantun firamare, sakandare da na gaba da sakandare a lokacin mulkinsa.

Haka zalika ya ce ya tura ɗalibai karatu zuwa jihohi da ƙasashe har 14 kuma, ya dauki malamai da kuma samar da wadatattun kayan aiki.

Kwankwaso ya zargi Ganduje da ruguza ilimi

Sanata Kwankwaso ya yi zargin cewa daga lokacin hawan Abdullahi Ganduje harkar ilimi duk ta lalace.

Ya ce makarantu sun rushe, ba a dauki malamai ba, an daina tura dalibai karatu, an sayar da filayen makarantu duk cikin shekaru takwas.

Abba ya fara ƙoƙarin kan ilimi inji Kwankwaso

Sai dai Rabi'u Kwankwaso ya ce abin farin ciki ne yadda Abba Kabir Yusuf ya fara dawo da darajar ilimi a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya yi wa Ganduje gugar zana yayin raba kayan miliyoyi a makarantu

Ya ce Abba Kabir Yusuf ya dauko hanyar farfaɗo da ilimi a dukkan kananan hukumomin Kano tare da samar da kayan aiki.

Kwankwaso ya karbi masu sauya sheka

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP a Najeriya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga yan Najeriya kan shigowa tafiyarsu domin kawo cigaba.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce sauya sheka da ake yi a Kano alama ce da ke nuna Abba Kabir Yusuf na aiki yadda ya kamata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng