Kungiya Ta Fadawa Tinubu Ribar da Zai Samu Idan Ya Sasanta Rikicin Masarautar Kano

Kungiya Ta Fadawa Tinubu Ribar da Zai Samu Idan Ya Sasanta Rikicin Masarautar Kano

  • Wata kungiyar 'yan Arewa mazauna Kudu ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya sanya baki a rikicin masarautar Kano da ya ki karewa
  • Shugaban kungiyar Alhaji Musa Saidu ya yi wannan kiran ne a babban birnin tarayya Abuja a wani taron manema labarai da ya kira
  • Alhaji Musa ya ce dambarwar sarautar alama ce ta rashin mutunta masarautar wanda bai kamata Tinubu ya yi gum da bakinsa a kai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar 'yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya ta yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya sa baki a rikicin masarautar Kano domin ceto masarautar daga tozarci.

Kungiyar ta ce ko kadan rikicin ba zai amfanar da jama’ar jihar Kano ba, haka kuma ba zai kari masarautar da komai ba sai ma rage kimarta a idon duniya.

Kara karanta wannan

'An kai mutumin da ya nemi Tinubu ya sauka daga mulki asibitin masu tabin hankali

Kungiyar 'yan Arewa mazauna Kudu sun yi magana kan rikicin masarautar Kano
Kungiyar 'yan Arewa ta bukaci Tinubu ya tsoma baki a rigimar masarautar Kano. Hoto: @masarautarkano, @officialABAT, @HrhBayero
Asali: Twitter

An nemi agajin Tinubu kan sarautar Kano

Shugaban kungiyar Alhaji Musa Saidu ne ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Post ta rahoto Alhaji Musa Saidu ya bayyana cewa:

“Kano jijiya ce ta siyasar kasar nan, kuma shugaba Tinubu na bukatar jihar a wa’adinsa na biyu a 2027, don haka bai kamata ya bari rigimar sarautar da ke faruwa a yanzu ta ci gaba ba.”

"Rashin girmama masarauta ne" - Kungiya

Shugaban kungiyar 'yan Arewan ya ce shirun da Shugaba Tinubu ya yi a kan lamarin abin damuwa ne kuma kuskure ne.

"Abin da ke faruwa a masarautar Kano babban rashin mutunta doka da oda ne kuma rashin girmama masarautar gargajiyar ne.
"An samu 'yan siyasa da suka rika tsige sarakuna Arewa a cikin shekaru ukun da suka wuce wanda alama ce ta rugujewar al'ummarmu da al'adunsu."

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan siyasar Kudancin Najeriya da za su iya kalubalantar Tinubu a 2027

- Alhaji Musa Sa'idu

Kira ga Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado

Saidu ya shawarci Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammadu Sanusi II da su yi la’akari da irin barnar da wannan dambarwar ta yi wa masarautar da suke dawurwura a kanta.

Musa Saidu ya bayyana cewa, dambarwar da aka samu a masarautar Kano babban abin kunya ne ga jihar da ma kasar baki daya.

Rigimar sarauta: NNPP ta gargadi Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar NNPP ta shaidawa shugaba Bola Tinubu cewa rigimar masarautar Kano zai iya shafar siyasarsa a nan gaba a jihar.

Shugaban jam'iyyar NNPP a Kano, Hashimu Dungurawa ya ce rashin tsoma bakin Tinubu a rigimar masarautar zai iya ba shi matsala a zaben 2027 da ke tafe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.