An Kai Mutumin da Ya Nemi Tinubu Ya Sauka daga Mulki Asibitin Masu Tabin Hankali

An Kai Mutumin da Ya Nemi Tinubu Ya Sauka daga Mulki Asibitin Masu Tabin Hankali

  • Rundunar 'yan sandan Adamawa ta garzaya da wani matashi da ya nemi shugaba Bola Tinubu ya yi murabus zuwa asibitin mahaukata
  • A makon da ya gabata Abdullahi Mohammed mai shekaru 30 ya hau dogon karfe na wutar lantarki tare da barazanar aika kansa lahira
  • Abdullahi ya ce lallai sai Tinubu ya sauka daga mulki saboda tsadar rayuwa, lamarin da 'yan sanda ke ganin yana da tabin kwakwalwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa - Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta ce an kai mutumin da ya nemi shugaban kasa Bola Tinubu ya sauka daga kan mulki asibitin mahaukata da ke Yola.

A Juma'ar makon jiya ne Abdullahi Mohammed mai shekaru 30 ya hau dogon karfen wutar lantarki a Mayo-Belwa a matsayin adawa da tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Kara karanta wannan

Kungiya ta fadawa Tinubu ribar da zai samu idan ya sasanta rikicin masarautar Kano

'Yan sanda sun yi magana kan mutumin da ya nemi Tinubu ya yi murabus
An kai mutumin da ya nemi Tinubu ya yi murabus asitin masu tabin hankali. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Mai so Tinubu ya sauka ya na asibitin mahaukata

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya shaida wa jaridar Punch a ranar Juma’a cewa ana kan yi wa Abdullahi Mohammed gwajin tabin hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SP Nguroje ya bayyana cewa:

“Lokacin da ‘yan sanda daga Moyo-Belwa suka kubutar da Abdullahi Mohammed daga dogon karfen wutar lantarki mai karfin 33kv, an gano kwayoyi a tare da shi ciki har da wiwi.

Abin da ya yi ya nuna cewa ba a cikin hankalinsa yake ba don haka sai muka kai shi asibitin masu tabin hankali domin a duba lafiyar kwakwalwarsa."

Ya hau dogon karfe har sai Tinubu ya bar ofis

A daren ranar Asabar da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kubutar da Abdullahi Mohammed wanda ya hau dogon karfen wutar lantarki mai karfin kilowatt 33 a Mayo-Belwa.

Kara karanta wannan

'Ko shekaru 100 ka ba Tinubu bai san yadda zai yi da Najeriya ba'

Abdullahi Mohammed ya yi barazanar fadowa daga kan karfen ko kuma wuta ta ja shi idan har shugaba Bola Ahmed Tinubu bai sauka daga kan mulki ba.

Kasancewar matakin da Abdullahi ya dauka alama ce ta yana kokarin halaka kansa, rundunar 'yan sanda ta yi kokarin lallaba shi har ya sauko, inda aka cafke shi nan take.

"Kun san yunkurin kashe kai laifi ne a tsarin mulkinmu, don haka za mu gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike."

- A cewar SP Nguroje.

Dan majalisa ya caccaki Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa wakilin mazabar Ndokwa/Ukwani a majalisar wakilai, Hon. Nnamdi Nzechi ya ce Bola Tinubu ne ya jawo tsadar rayuwa.

'Dan majalisar ya ce gwamnatin Tinubu ta kawo tsare-tsaren da suka jefa 'yan kasar a mawuyacin hali ba tare da daukar matakan saukakawa al'umma ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.