Lambar Girma: Abba Ya Kere Dukkan Gwamnoni, Ya Zama Na 1 a Najeriya

Lambar Girma: Abba Ya Kere Dukkan Gwamnoni, Ya Zama Na 1 a Najeriya

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu lambar girmamawa inda aka zaɓe shi a matsayin mafi dacewa
  • A bisa zaben Abba Kabir Yusuf da aka yi, hakan na nuni da cewa gwamnan Kano ya sha gaban dukkan gwamnoni
  • Al'ummar jihar Kano musamman a kafafen sadarwa sun taya Abba Kabir Yusuf murna tare da masa fatan cigaba da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano ya samu lambar girmamawa daga wani kamfanin jarida a Afrika.

Biyo bayan samun lambar yabon, al'umma da dama a Kano sun taya Abba Kabir Yusuf murna tare da masa fatan alheri.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta raba kanta da rancen €64m da Ganduje ya laftowa Kano a 2018

Abba Kabir Yusuf
An ba Abba Kabir lambar girma. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan karrama Abba Kabir Yusuf ne a cikin wani sako da Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ba Abba Kabir lambar yabo

Kamfanin jaridar Africa Trust Magazine ya zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin na daya a cikin gwamnonin Najeriya kan jajircewa da yin ayyuka.

A yau Alhamis, daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ta fitar da sanarwa kan lambar girmar. Ga abin da yake cewa:

Abba Kabir Yusuf ya samu lambar girma bisa kasancewa gwamna mafi dacewa na wannar shekarar daga African Trust Magazine

- Sanusi Bature Dawakin-Tofa, daraktan yada labaran gwamnatin Kano

Mutanen Kano sun taya Abba murna

Mutanen Najeriya sun taya Abba Kabir Yusuf murna musamman a karkashin rubutun da Sanusi Bature ya yi.

Wani mai amfani da kafar Facebook, Musa Mudi ya taya gwamnan murna inda ya ce yana masa fatan cigaba da yin ayyuka na musamman a jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu, gwamnoni sun yi ta'aziyyar uwar gidan gwamnan Akwa Ibom

Haka zalika Auwal M Yakasai ya yi addu'ar Allah ya cigaba da ba gwamna Abba kariya domin cigaba da ayyuka na kwarai.

BUK ta karrama Abba Kabir Yusuf

A wani rahoton, kun ji cewa jami’ar Bayero ta Kano ta karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa namijin kokarinsa na daga darajar ilimi a jihar.

An ruwaito cewa makarantar ta karrama gwamna Abba Kabir Yusuf ne a bikin karramawa da yaye dalibai karo na 38 da ya gudana a jami'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng