Yan Sanda Sun Mutu bayan Yan Bindiga Sun Cilla Musu Bam, An Dauki Mataki Mai Tsauri

Yan Sanda Sun Mutu bayan Yan Bindiga Sun Cilla Musu Bam, An Dauki Mataki Mai Tsauri

  • Rundunar yan sandan reshen jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar wasu jami'anta bayan harin yan bindiga
  • Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga shi ya tabbatar da haka ga yan jaridu inda ya ce sun rasa jami'ansu guda biyu
  • Lamarin ya faru ne da safiyar yau watau Alhamis 3 ga watan Oktoban 2024 a karamar hukumar Nnewi da ke jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Wasu yan bindiga sun hallaka jami'an yan sanda a jihar Anambra da ke Kudancin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Alhamis 3 ga watan Oktoban 2024 a Uruagu da ke karamar hukumar Nnewi.

Yan bindiga sun yi ajalin jami'an yan sanda guda 2
Yan bindiga sun hallaka yan sanda 2 a jihar Anambra. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda yan bindiga suka hallaka yan sanda

Kara karanta wannan

Ana fargabar jami'an tsaro sun tarwatsa masu kada kuri'a, sun kwace kayan zaben

Kakakin rundunar yan sanda, Tochukwu Ikenga shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da aka turawa Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ikenga ya ce miyagun sun yi ta harbi ta ko ina bayan hango jami'an tsaron na tunkararsu.

Ya ce yan bindigan sun jefa abin fashewa cikin motar yan sandan wanda ya yi ajalin guda biyu daga cikinsu.

"Bayanan farko da muka samu sun ce miyagun sun yi ta harbi bayan ganin motar jami'an tsaro inda suka jefa musu bam cikin motarsu."
"Dalilin haka, biyu daga cikin jami'an tsaron sun rasa ransu bayan motar ta kama da wuta."

- Tochukwu Ikenga

Rundunar yan sanda ta ba al'umma shawara

Ikenga ya ce tuni rundunar ta bazama domin zakulo wadanda suka aikata hakan domin fuskantar hukunci.

Ya bukaci al'umma da su cigaba da ba su hadin kai na bayanai domin dakile hare-haren yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da babban ɗan siyasa da wani shugaban al'umma a Najeriya

An yi shekaru 3 da sace 'dan takarar gwamna

Kun ji cewa a ranar 18 ga watan Satumbar 2021 aka sace dan takarar gwamna a jam'iyyar LP a jihar Anambra, Obiora Agbasimalo.

Agbasimalo a yanzu haka ya shafe shekaru uku kenan babu labarinsa ko kuma wani bayani game da halin da ya ke ciki.

Lamarin ya faru ne yayin da dan takarar ke kamfe a kokarin neman mulki a Luli da ke karamar hukumar Ihiala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.