Karshen Alewa: Yan Ta'adda Sun Ji Wuta, Sun Shiga Hannun Yan Sanda a Abuja
- Rundunar yan sanda ta bayyana kama wasu hatsabiban yan ta'adda da su ka addabi Abuja da wasu jihohin Arewa
- Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar a Abuja, SP Josephine Adeh ta ce an kama mutane hudu a maboyarsu da ke birnin
- Daga cikin abubuwan da aka gano daga miyagun masu garkuwa da mutanen akwai bindigar AK-47 da alburusai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Jami'an rudunar yan sandan kasar nan ta bankado maboyar yan ta'adda a yankin Sauka, a hanyar tashar jirgin sama da ke Abuja.
Yan sandan sun yi nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane, ciki har da wani tsohon mai laifi Yau Sani, da Nuhu, sai Kabiru Muhammed da Yusuf Hassan.
FCT Police Command ta wallafa a shafinta na X cewa kakakin rundunar yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ce ta tabbatar da yan ta'addan na daga cikin bata-garin da su ka addabi mazauna Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano maboyar yan ta'adda
Jaridar Leadership ta wallafa cewa kakakin rundunar yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ta bayyana cewa a ranar zagayowar yancin kan kasar nan ne aka gano maboyar yan ta'addan.
Ta ce bayan jami'ansu sun samu rahoton sirri kan ayyukan yan ta'addan ne su ka bibiye su har aka kai ga gano inda su ke.
Yan ta'adda sun amsa laifin satar jama'a
Rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana cewa mutane hudu da aka kama a Abuja sun amsa laifin satar mutane da dama a Abuja da kewaye.
Matasan hudu sun ce sun kai hare-hare yankunan Dakwa, Dawaki, Rukunin gidajen Aco, Dupe Village Zuma Rock, kauyen Kuchiko da wasu kauyukan a jihohin Kaduna da Neja.
Haka kuma an yi nasarar kwato bindigar AK-47 da alburusai da dama daga hannunsu.
'Yan sanda sun kama dan ta'adda
A wani labarin kun ji cewa rundunar yan sandan Jigawa ta bayyana cewa an kama wasu miyagun yan ta'adda da su ka addabi mazauna jihar da fashi da makami.
Dan fashin da aka kama, wanda ake zargin ya addabi mazauna kananan hukumomin Ringim da Dutse a Jigawa, ya shaidawa yan sanda wurin da ya ke sayo makamai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng