‘Ku Zauna a Shirye,’ NLC Ta Yi Zazzafan Gargadi a Dukkan Jihohi kan Karin Albashi

‘Ku Zauna a Shirye,’ NLC Ta Yi Zazzafan Gargadi a Dukkan Jihohi kan Karin Albashi

  • Kungiyar kwadago ta kara daukar zafi kan maganar karin mafi ƙarancin albashin ma'aikata zuwa N70,000 a Najeriya
  • Shugaban kwadago, Joe Ajaero ya ce suna shirye kan ɗaukar mataki a dukkan jihohin Najeriya da suka gaza kara albashi
  • Ajaero ya yi bayanin ne yayin wani taron yan kwadago kan tsara yadda za a fara biyan sabon albashi a Kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Kungiyar kwadago ta fitar da gargadi a dukkan jihohin Najeriya kan maganar ƙarin albashi zuwa akalla N70,000.

Joe Ajaero ya bukaci shugabannin kwadago su zauna cikin shiri a ko ina domin daukar mataki kan jihar da ta gaza karin albashi.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Yan kwadago
Yan kwadago sun yi sabon gargadi a jihohi. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Joe Ajaero ya ce za su cigaba da gwagwarmaya kan tabbatar da walwalar ma'aikata a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashi: NLC ta yi gargadi a dukkan jihohi

Shugaban yan kwadago, Joe Ajaero ya gargadi gwamnonin jihohi da ma'aikatu masu zaman kansu kan karin albashin ma'aikata.

Joe Ajaero ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar mataki mai tsauri kan duk wata jiha da ta gaza biyan albashin ma'aikata na N70,000.

A karkashin haka, shugaban ya bukaci yan kwadago su zauna cikin shirin ko-ta-kwana domin daukar mataki a kan dukkan jihar da ta gaza karin albashi.

NLC ta ce nauyi ya yi wa ma'aikata yawa

Joe Ajaero ya ce ma'aikata na fama da nauyin ciyar da iyalansu, sanya su a makaranta da kuma wasu ayyuka domin al'umma.

Saboda haka Ajaero ya ce kudin da suke nema a biya ma'aikata bai taka kara ya karya ba kuma ga al'umma yake tafiya domin kullum a cikin hidima suke.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da murnar ranar ƴanci: Gwamnatin tarayya ta karawa ƴan fansho albashi

Shugaban kwadago ya ce za su cigaba da gwagwarmaya kan tabbatar da ma'aikata sun samu walwala domin NLC ce gatansu a Najeriya.

Tinubu ya yi karin albashi a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000.

Hakan na zuwa ne watanni bakwai bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng