‘Ba Mu Yarda ba,’ Yan Majalisa Sun Ja da Tinubu kan Shugabansu

‘Ba Mu Yarda ba,’ Yan Majalisa Sun Ja da Tinubu kan Shugabansu

  • Yan majalisar wakilai sun nuna kin amincewa da lambar girma ta CFR da Bola Tinubu ya ba shugabansu, Abbas Tajudeen
  • Yan majalisar sun bayyana cewa ba za su yarda da nuna bambanci tsakanin shugabansu da shugaban majalisar dattawa ba
  • A ranar Talata ne aka fitar da sanarwa kan lambar girma da shugaban kasa zai ba wasu manyan mutane ciki har da Abbas Tajudeen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yan majalisar wakilai sun nuna kin amincewa da lambar girma da shugaban kasa Bola Tinubu zai ba shugabansu.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabi shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen domin ba shi lambar yabo ta CFR.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya damu da matasa, ya shirya yin taron kasa na kwanaki 30

Bola Tinubu
Majalisa ta yi watsi da lambar yabo da aka ba shugabanta. Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar the Cable ta wallafa cewa a zaman majalisar wakilai na ranar Laraba ne yan majalisar suka yi watsi da hukuncin shugaban kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai ba mutane lambar girma

A ranar Talata shugaban kasa ya zabi mutane da dama ciki har da shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen domin ba su lambar girma ta CFR.

Haka zalika Bola Tinubu ya zabi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio domin ba shi lambar yabo ta GCON.

Yan majalisa sun ja da Tinubu

Yan majalisar wakilai sun nuna kin amincewa da hukuncin da shugaba Bola Tinubu ya yi kan ba Abbas Tajudeen lambar yabo ta CFR.

Punch ta wallafa cewa yan majalisar wakilai sun ce bai kamata a ba shugabansu lamabar girma ta CFR ba kuma a ba shugaban majalisar dattawa lambar girma ta CGON.

Dan majalisar wakilai daga jihar Benue, Philip Agbese ne ya kawo kudirin gaban majalisar kafin su amince tare da tabbatar da shi.

Kara karanta wannan

Oktoba: An fadawa Tinubu sirrin shawo kan matasa masu shirin zanga zanga

A halin yanzu dai kallo ya koma kan fadar shugaban kasa domin ganin matakin da za ta dauka kan abin da ya faru a majalisar na kin amincewa da hukuncin Bola Tinubu.

Tinubu zai tafi hutu London

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya domin tafiya hutu kasar Birtaniya a yau Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar zai tafi hutun ne na tsawon mako biyu domin yin nazari kan tsare tsaren tattalin arziki da ya kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng