NiMet: Za a Zabga Ruwan Sama daga Laraba zuwa Juma'a a wasu Jihohin Arewa 16
- Ana sa ran za a sha mamakon ruwan sama tare da tsawa daga ranar Laraba zuwa Juma'ar makon nan a wasu jihohi 16 na Arewa
- Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa ruwan zai sa a lokuta daban daban a wadannan jihohi
- Jihohin da ake sa ran za su samu ruwan saman sun hada da Adamawa, Taraba, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Kaduna da dai sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a zabga ruwan sama hade da tsawa daga ranar Alhamis zuwa Asabar a wasu jihohin kasar nan.
A yayin da ruwan saman zai sauka da safiyar ranakun uku, NiMet ta ce wasu jihohin za su samu nasu ruwan ne da yammacin kowace rana.
An fitar da hasashen yanayi na NiMet a ranar Talata, 1 ga watan Oktobar 2024 a Abuja kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ruwan sama a ranar Laraba
NiMet ta yi hasashen ruwan sama da tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Kaduna a safiyar Laraba.
A cewar NiMet, ana sa ran za a yi ruwa da tsawa da yammacin Laraba a wasu sassan jihohin Bauchi, Adamawa, Kaduna, Katsina, Taraba, Yobe, Zamfara, Borno da Kebbi.
“A shiyyar Arewa ta tsakiya, ana hasashen ruwa da tsawa a sassan babban birnin tarayya, jihohin Neja, Nasarawa da Binuwai da safe.
“Da yammaci kuwa, ana sa ran za a yi ruwa da tsawa a babban birnin tarayya, jihohin Neja, Kogi, Kwara, Benuwai, Filato da Nasarawa."
- A cewar hasashen.
Ruwan sama a ranar Alhamis
Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwa da tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba da Kebbi da safiyar ranar Alhamis.
An yi hasashen za a yi ruwa da tsawa a wasu sassan jihohin Kaduna, Adamawa, Katsina, Kebbi, Taraba, Sokoto da Zamfara a yammacin ranar.
“A yankin Arewa ta tsakiya, ana iya samun ruwa da tsawa a sassan babban birnin tarayya, jihohin Neja, Kogi, Kwara, Benuwai da Nasarawa da safe.
“Yayin da kuma daga takewar rana har zuwa yammaci ake sa ran za a yi ruwa da tsawa a sassan babban birnin tarayya, jihohin Neja, Kogi, Benuwai da Nasarawa.
- A cewar NiMet.
Ruwan sama a ranar Juma'a
A cewar NiMet, ana sa ran za a yi ruwa da tsawa a sassan jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi da safiyar ranar Juma'a.
NiMet ta ce:
“A yankin Arewa ta tsakiya ana sa ran saukar ruwa da tsawa a sassan Nasarawa, Kogi, Kwara, Neja da kuma babban birnin tarayya da safe.
“A yammacin ranar, ana sa ran za a yi ruwa da tsawa a sassan Nasarawa, Kogi, Benuwai, Kwara, Neja da kuma babban birnin tarayya."
Ruwan sama a Kano da jihohi 16
A wani rahoton makamamancin wannan, mun ruwaito cewa hukumar NiMET ta sanar da cewa za a tafka mamakon ruwa a jihohi 17 na Arewa.
Hukumar ta gargadi mazauna wadannan jihohi da su yi taka tsantsan musamman wadanda ke a yankunan gabar tekuna domin gujewa ambaliyar ruwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng