Ana Tsaka da Murnar Ranar Ƴanci: Gwamnatin Tarayya Ta Karawa Ƴan Fansho Albashi

Ana Tsaka da Murnar Ranar Ƴanci: Gwamnatin Tarayya Ta Karawa Ƴan Fansho Albashi

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ma'aikatan da suka yi ritaya daga aikin gwamnati za su samu karin kudin fansho da N32,000
  • Gwamnatin ta bakin hukumar NSIWC ta ce karin kudin fanshon ya biyo bayan aiwatar da sabon mafi karancin albashi da aka yi
  • Ga hukumomin da karin bai shafi tsofaffin ma'aikatansu ba, NSIWC ta nemi su tuntubeta domin sanin matsayin albashin 'yan fanshon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar da kara kudin fansho na tsofaffin ma'aikatan kasar nan.

Biyo bayan aiwatar da sabon sabon mafi karancin albashi, yanzu ma'aikatan da suka yi ritaya za su samu karin N32,000 a cikin kudaden fanshonsu na wata-wata.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 7 daga jawabin Tinubu na ranar samun 'yanci

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan karawa ma'aikatan da suka yi ritaya albashi
Gwamnatin tarayya ta karawa tsofaffin ma'aikata kudin fansho da N32,000. Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

An karawa 'yan fansho albashi

Hakan ya fito ne a cikin wata takarda da hukumar kula da albashi da kudin shiga ta kasa da jaridar Punch ta gani a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar takardar, mai kwanan wata 27 ga Satumba, 2024 dauke da sa hannun shugaban NSIWC, Ekpo Nta:

"Wadanda abin ya shafa sun hada da wadanda suka yi ritaya a karkashin tsarin albashi na likitoci, ma’aikatan lafiya, malamai, ‘yan sanda, jami’an tsaro, sojoji, da sauran su."
“An amince da fara biyan karin albashin ta fara aiki daga ranar 29 ga Yuli, 2024."

Gwamnati ta aika sako ga hukumomi

Hukumar NSIWC ta ce ma'aikatun da ba sa a cikin rukunonin da wannan karin ya shafa za su tuntubi hukumar domin sanin matsayin karin albashin tsofaffin ma'aikatansu.

Jaridar The Guardian ta rahoto wani bangare na sanarwar da ke cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin shiyya: An samu baraka tsakanin sanatoci kan bitar kundin tsarin mulki

"Bisa ga sashe na 173 (3) na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da sashe na 3 (P) na dokar NSIWC, hukumomin da ba sa cikin wadanda aka ambata za su iya tuntubar hukumar game da karin albashin tsofaffin ma'aikatansu."

Kwamitin gyaran albashi ga ma'aikatan gwamnati ya gana a ranar Juma'a inda ya amince da fara aiwatar da sabon albashin ma'aikata na N70,000.

Tinubu zai aiwatar da sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta fara aiwatar da sabon albashin N70,000 daga watan Yulin 2024.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnati da kungiyar kwadago suka rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna kan sabon mafi karancin albashin N70,00.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.