Asiri Ya Tonu bayan Sace Jariri Dan Kwanaki 7 a Gidan Suna

Asiri Ya Tonu bayan Sace Jariri Dan Kwanaki 7 a Gidan Suna

  • Rundunar yan sanda a jihar Nasarawa ta tabbatar da cafke wata mata da ake zargi da satar jariri dan kwanaki bakwai da haihuwa
  • Kakakin yan sanda a jihar Nasarawa, Ranham Nansel ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Keffi yayin da ake taron suna
  • Haka zalika rundunar yan sandan ta kama wani mutum da ake zargi da satar babur inda aka kwato abubuwan hawa a wajensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa ta kama wata mata da ake zargi da satar jariri.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa a ranar 28 ga Satumba.

Kara karanta wannan

An kama dan fashin da ya addabi mutane, ya tona inda ya sayo makamai

Yan sanda
An kama wacce ta sace jariri ana sunansa a Nasarawa. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa matar da ake zargin ta yi dabara ne ta shiga gidan sunan kafin asirinta ya tonu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama mai satar jariri a gidan suna

Rahotan rundunar yan sanda ya tabbatar da cewa an kama wata mata mai suna Khadija Aliyu da zargin sace jariri a gidan suna.

Punch ta wallafa cewa ana zargin Khadija Aliyu ne da sace jaririn yayin da ake tsaka da bikin sunansa a karamar hukumar Keffi.

Yadda aka so sace jariri ranar suna

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa matar da ake zargin ta shigo gidan sunan ne bayan ta yi ciko a cikinta wanda hakan zai nuna alamar tana da ciki.

Ana tsaka da bikin sunan ne sai matar ga siɗaɗe ta shiga cikin daki ta sace jaririn a kan gado ta boye a lullubinta amma tana kokarin fita aka kama ta.

Kara karanta wannan

Mota ta markaɗe yan Maulidi, wasu sun rasu, da dama sun samu raunuka

...An kama barawon babur a Nasarawa

Rundunar yan sanda ta kara bayyana cewa ta kama wani matashi mai suna Hussaini Muhammad da ake zargi da satar babur.

Bayan kama Hussaini, an samu babur guda uku da ake zargin cewa sato su aka yi kuma dama an taba kulle shi a kurkuku kan sata.

Jami'an tsaro sun kama dan fashi a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya a jihar Jigawa ta sanar da kama wasu yan fashi da makami da suka addabi al'ummar Arewa.

Cikin miyagun da rundunar ta kama, har da babban ɗan fashi da makami da ya addabi mutane a jihar Jigawa da wasu sassan yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng