Dubun wata mata dake satar jarirai a Asibiti ya cika A Kaduna

Dubun wata mata dake satar jarirai a Asibiti ya cika A Kaduna

An samu yamutsi a Asibitin Yusuf Dantsoho dake jahar Kaduna, wanda akafi sani da suna Asibitin Dutse dake unguwar Tudun Wada, a Asabar 3 ga watan Nuwamba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan yamutsi ya faru ne sakamakon cafke wata mata da ta saci wani jariri dan wata Tara da haihuwa.

Rahotanni sun tabbatar da faruwar wannan lamari, inda suka ce an kama matar ne da misalin karfe 10 na safiyar asabariyar data gabata.

KU KARANTA: Abu namu: Buhari zai gina kwalejin horas da matuka jirgin sama a jahar Katsina

Jaridar Daily Trust ta ruwaito jama'a sun kama matar ne bayan ta yi awon gaba da jaririn daga sashin kananan yara na Asibitin, wanda aka ce mara lafiya ne.

Kiris ya rage jama'a su halaka wannan mata bayan mahaifiyar jaririn ta yi kuwwa tare da neman agajinsu a kokarinta na ceto jaririnnata.

Bugu da kari, shugaban ma'aikatan jinya na Asibitin, Jamila Garba ta tabbatar da faruwar lamarin.

Zuwa yanzu dai jami'an tsaron Asibitin sun mika barauniyar zuwa ofishin Yansandan Metro dake makwabtaka da Asibitin.

A wani labarin kuma wani matashi Mathias Geoffrey da rikicin jahar Kaduna ta rutsa da shi ya samu sauki har ma ya kai ma gwamnan jahar ziyara a ofishinsa.

Mathias mai shekaru 23 ya kai ma Gwamna El-Rufai ziyarar ne don ya gode masa bisa kulawar da ya nuna masa a lokacin da yake jinya a Asibiti.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: