Mota Ta Markaɗe Yan Maulidi, Wasu Sun Rasu, da dama Sun Samu Raunuka
- An samu mummunan haɗarin mota da ya ritsa da yan Maulidi a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa a Arewacin Najeriya
- Bayanai sun nuna cewa matukin wata mota ne ya haura kan mutane suna tafiya yayin bikin Maulidi kuma ya kashe wasu daga cikinsu
- Rundunar yan sandan Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin kuma kwamishinan yan sanda ya tura sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Al'umma sun shiga jimami a karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa bayan hadarin mota ya ritsa da yan Maulidi.
Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta fara gudanar ga bincike domin gano abin da ya jawo haɗarin.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ne ya tabbatarwa Legit faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mota ta haura kan yan maulidi a Jigawa
Rahoton da rundunar yan sanda ta fitar ya nuna cewa wani matukin mota da ya fito daga Yobe ya haura kan masu Maulidi a karamar hukumar Ringim.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daidai yankin Gagarawa yayin da motar ta kubuce daga hannun matukin.
Yan Maulidi sun rasu a haɗarin motan
Legit ta gano cewa motar ta haura kan yan Maulidi mutum 15 ne yayin da suke tafiya a gefen hanya.
A sakamakon haka, motar ta kashe yan Maulidi shida yayin da mutum tara suka samu munanan raunuka.
Hadarin Maulidi: Yan sanda za su yi bincike
Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da bincike domin gano dalilin hadarin da ɗaukan matakin da ya dace.
Haka zalika kwamishinan yan sandan jihar, CP AT Abdullahi ya yi jaje ga iyalan waɗanda suka rasu tare da addu'ar Allah ya ji kansu.
Buhari ya yi jajen yan Maulidi
A wani rahoton, kun ji cewa mutane a Najeriya sun nuna alhini sakamakon wani hadarin mota da ya jawo mutuwar yan Maulidi a Kaduna.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shiga cikin sahun mutanen da suka nuna damuwa kan rasa rayuka da aka yi a hadarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng