Najeriya @64: Gwamna Ya Lissafo Ni'imomi 3 a Najeriya, Ya Nemi a Dage da Addu'a

Najeriya @64: Gwamna Ya Lissafo Ni'imomi 3 a Najeriya, Ya Nemi a Dage da Addu'a

  • Gwamna Hope Uzodinma ya taya al'umar kasar Najeriya murnar cika shekaru 64 da samun yancin kai
  • Gwamnan ya ce akwai ni'imomi da Ubangiji ya yi wa kasar nan masu tarin yawa, saboda haka ya dace a yi murna
  • Amma ya na ganin akwai bukatar mazauna kasar nan su canja hali idan har ana son a samu karin nasarori

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce babu abin da yan kasar nan za su yi sai godiya ga Mahallicci da ya nuna masu zagoyar samun yancinta.

Gwamnan Imo ya fadi haka ne a wani coci da ke Owerri, yayin da ake addu'a kan cikar Najeriya shekaru 64 da samun yancin kai daga turawa.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya kare manufofin gwamnati, ya jaddada alfanun cire tallafin fetur

Uzodinma
Gwamna ya taya yan Najeriya murnar cika shekaru 64 da yanci Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Uzodinma ya ce dadi da cigaban kasa na nan tafe, inda ya ke da yakinin kasar nan za ta samu daukakar da ta dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya @64: Gwamnan Imo ya ta ya kasa murna

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa gwamna Hope Uzodinma ya ce akwai manyan abubuwan da aka albarkaci kasar nan da su cikin shekaru 64.

Ko da ba yadda aka so ba, gwamnan na ganin ana samun cigaba sannu-sannu, kasar ba ta fada cikin yakin gama-gari ba, sannan Allah Ya raya kasar da mazauna cikinta.

Gwamna Uzodinma ya nemi a sauya hali

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce dole sai yan kasar nan sun sauya halayensu zuwa na gari kafin a samu nasarorin da ake bukata.

Ya shawarci jama'a su sauya tunanin kan lalata kadarorin gwamnati da tayar da hankulan jama'a domin a cimma nasarorin da kasar ta ke fatan cimmawa.

Kara karanta wannan

Kaduna: An zargi sojoji da sake jefa bama bamai a masallaci aka kashe bayin Allah

1 Oktoba: An shirya tsaron yan kasa

A baya mun ruwaito cewa rundunar yan sandan jihar Yobe ta shirya kare rayuka da dukiyoyin jama'a gabanin zagoyar samun yancin kan kasar nan da zai gudana a ranar Talata.

Kwamishinan yan sandan jihar, Garba Ahmed ya shawarci sarakuna da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran jama'ar gari da su bayar da hadin kai wajen tsaron lafiyarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.