An Shiga Tashin Hankali a Zamfara, wani Direban Mota Ya Kashe Mutane 6 Ƴan Gida 1

An Shiga Tashin Hankali a Zamfara, wani Direban Mota Ya Kashe Mutane 6 Ƴan Gida 1

  • Wani mummunan hatsari ya faru a garin Gusau da ke jihar Zamfara inda wani direban motar daukar yashi ya murkushe mutane
  • An rahoto cewa wani magidanci ne ke tafiya da matarsa da kuma yaransu hudu a lokacin da motar ta kwace ta murkushe su kan titi
  • Wani ganau ya bayyana cewa motar ce ta kwacewa direban sakamakon abin da ya ke tunani da matsalar birki, ya kashe mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Mutanen Gusau sun shiga cikin tashin hankali yayin da wani direban motar daukar yashi ya murkushe wasu 'yan gida daya su shida.

An rahoto cewa direban motar tifar ya yi ajalin miji da mata tare da 'ya'yansu hudu a garin Gusau da ke jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Kaduna: An zargi sojoji da sake jefa bama bamai a masallaci aka kashe bayin Allah

Direban motar yashi ya halaka mutane 6 'yan gida 1 a Zamfara
"Yan gida daya su 6 sun mutu bayan direban mota ya murkushe su a Zamfara.
Asali: Original

Mota ta halaka 'yan gida guda

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin 'yan sandan Zamfara, SP Yazid Abubakar ya ce mutanen shida sun mutu nan take, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce wadanda suka mutu sun hada da kananan yara hudu, miji da kuma matarsa.

"Ba zan iya ba da bayani kan ko yaran maza ne ko mata ba, amma dai su hudu ne. Ya zuwa yanzu mun cafke direban kuma muna kan yin bincike."
"Da zarar mun kammala bincike za mu sanar da al'umma halin da ake ciki, amma a yanzu zan iya yin magana kan wadanda hatsarin ya shafa ne kawai."

- A cewar SP Yazid.

Yadda hatsarin motar ya afku

An rahoto cewa motar ta kwacewa direban ne tare da afkawa wani mutumi da ke tafiya kan babur tare da iyalansa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa kauyen Ministan tsaro, sun sace 40 da hallaka wasu

Shaidar gani da ido ya ce dukkanin mutanen shida da ke kan babur din sun mutu nan take bayan da direban motar ya murkushe su.

"Lamari ne mai ban tsoro. A idonka a ce ka ga miji da mata da dukkanin 'ya'yansa sun mutu a irin wannan yanayi, abin tsoro ne. Na sharbi kuka ganin wannan hatsari."

- A cewar wani ganau.

Ya kuma yi zargin cewa birkin motar ne ba shi da kyau yana mai cewa "da ace birkin na da kyau da direban ya iya tsayar da motar kafin murkushe mutanen."

Ya ce da yawan tifofin da ake aiki da su a yankin ba su da lafiyar birki, haka nan dai direbobi ke hawa hanya da su.

Mota ta kashe mutane 4 a Zamfara

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa wata motar tirela da ke tafiya da baya ta murkushe mutane hudu ciki har da mace mai shayarwa.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya yi ajalin mace mai shayarwa da wasu mutane 3 a Zamfara

An rahoto cewa direban motar ya tsere bayan ganin irin aika aikar da yayi inda daga bisani hukumar kiyaye hadurra ta kwashe gawarwarkin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.