Katuwar Mota Ta Latse Mai ‘ya ‘ya 30 da Fasinjansa, Sun Zarce Barzahu Nan-take

Katuwar Mota Ta Latse Mai ‘ya ‘ya 30 da Fasinjansa, Sun Zarce Barzahu Nan-take

  • Wani Bawan Allah mai suna Abdulsalam Ibrahim da yake acaba ya gamu da ajalinsa a hadarin mota
  • Tifa ta buge Dattijon da wani fasinja da ya dauko, dukkansu sun mutu yayin da mai mota ya tsere
  • Hukumar FRSC mai kula da titunan Najeriya sun tabbatar da wannan mummunan hadari a yau

Kogi - Hukumar FRSC mai kula da titunan Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani magidanci wanda katuwar mota ta murkushe a Lokoja, jihar Kogi.

Rahoton da Daily Trust ta fitar dazu, ya bayyana cewa Abdulsalam Ibrahim yana kan babur, motar tifa mai daukar kasa ta bi takan shi a yankin Ganaja.

Babban jami’in FRSC na jihar Kogi, Stephen Dawulung ya shaidawa manema labari cewa Marigayin mai shekara 60 ya mutu ya bar ‘ya ‘ya 30 a Duniya.

Kara karanta wannan

Farashin Man fetur: Har Yau Ba Mu Kara Sisin Kobo Kan N165 ba Inji Gwamnati

Kamar yadda Stephen Dawulung yayi bayani, wannan katuwar mota ta kashe Abdulsalam Ibrahim wanda ‘dan acaba ne da kuma fasinjan da ya dauko.

Hukumar ta bayyana wannan mutuwa a matsayin abin takaici da tashin hankali, ganin an rasa rayuwa biyu da rayuka fiye da 30 da suka dogara da su.

Zuwa yanzu Legit.ng Hausa ba ta samu labarin sunan fasinjar da ya mutu tare da dattijon ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Katuwar Mota
Hoton wata Tifa (dabam) Hoto: nigeriantech.com.ng
Asali: UGC

Yadda abin ya faru - FRSC

“Wanda ya jawo wannan hadari ya tsere, domin a lokacin da aka kira mu domin mu bada agaji, ba a iya iske direban da tifarsa ba.
Wadanda suka shaida hadarin da idanunsa sun bayyana mana cewa direban tifar ya tsere nan take bayan ganin abin da ya auku.
A haka direban ya bar gawan wadannan Bayin Allah a titi a hannun masu tausayi."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Abuja, Sunyi Awon Gaba Da Mutane a Gona

- Stephen Dawulung

An ajiye gawawwaki a asibiti

Dawulung yace jami’an FRSC sun ajiye gawan wannan mutumi da na fasinjan da suka mutu tare a wurin ajiye gawawwaki a asibitin Ankuri da ke Lokoja.

Shugaban kungiyar ‘Yan acaba na jihar Kogi, Malam Musa Baba-Aliyu ya fadawa jaridar cewa wanda ya riga mu gidan gaskiyar mutumin jihar Katsina.

Ibrahim ya gamu da ajalinsa ne yana yunkurin kaucewa direban Keke Napep da ya auko masu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel