Ministan Tinubu Ya Kare Manufofin Gwamnati, Ya Jaddada Alfanun Cire Tallafin Fetur

Ministan Tinubu Ya Kare Manufofin Gwamnati, Ya Jaddada Alfanun Cire Tallafin Fetur

  • Ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, Atiku Bagudu ta bayyana cewa cire tallafin fetur zai amfani kasar nan
  • Atiku Bagudu, wanda tsohon gwamnan Kebbi ne ya ce shugaba Bola Tinubu ya damu matuka da halin da kasa ke ciki
  • Ya ce daga tsare-tsaren da shugaban kasa ke yi akwai na tabbatar da cigaban tattalin arziki mai dorewa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu duk da koken yan Najeriya.

Daga cikin manufofin da tsohon gwamnan ya kare har da cire tallafin man fetur, lamarin da yanzu ya jawo hauhawar farashin ababen hawa da kayan masarufi.

Kara karanta wannan

'Wahala za ta kare', Minista ya fadi yadda Tinubu ke kokarin dakile halin kunci

Tinubu
Gwamnatin tarayya ta kare manufofinta kan Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa dukkanin matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka, ana bukatarsu wajen inganta tattalin arzikin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista ya fadi alfanun cire tallafin fetur

Minista Atiku Bagudu ya ce dole ce ta sa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu cire tallafin man fetur, kamar yadda ya bayyana a jawabin da hukumar wayar da kai ta NOA ta wallafa.

Ministan ya kara da bayyana muhimmancin jama'a su koma da samfurin CNG na iskar gas domin ya fi arha da tsafta da lafiyar ababen hawa.

Ministan kasafi ya fadi ayyukan gwamnati

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai tsare-tsare karkashin shirinta na farfado da kasar nan wajen magance matsalolinta sannu a hankali.

Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya kara da cewa Bola Tinubu na daukar matakan da za su tabbatar da cigaban tattalin arzikin mai dorewa.

Kara karanta wannan

Bayan zarginta da jefa jama'a a wahala, gwamnati ta fadi alfanun cire tallafin fetur

"Wahala za ta kare:" Ministan Tinubu

A baya mun ruwaito cewa karamin Ministan muhalli a Najeriya, Iziaq Kunle Salako ya yi wa yan Najeriya albishir da cewa wahalar da ake fuskanta a kasar nan za ta wuce.

Karamin Ministan ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na bakin kokarinsa wajen ganin an shawo kan matsalolin da su ka addabi jama'ar kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.