Tinubu Ya Kinkimo Bashin $1.57bn daga Bankin Duniya, za a yi Muhimman Ayyuka 3

Tinubu Ya Kinkimo Bashin $1.57bn daga Bankin Duniya, za a yi Muhimman Ayyuka 3

  • Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kara kinkimo bashin $1.57bn daga bankin duniya domin ayyuka na musamman a kasar nan
  • An ruwaito cewa Bankin Duniya ya amince da ba gwamnatin tarayya bashin ne domin yin ayyuka na musamman guda uku a Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar 26 ga watan Satumba ne Bankin Duniya ya amince da ba gwamnatin Bola Tinubu bashin kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu bashin $1.57bn daga Bankin Duniya.

Bankin Duniya ya bayyana cewa tun a ranar 26 ga Satumba ne ya amince da ba gwamnatin tarayya bashin.

Kara karanta wannan

NAGGMDP: Likitoci za su tsunduma yajin aiki a jihar Kano, bayanai sun fito

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya karbo bashi daga Bankin Duniya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa an karbo bashin ne domin gudanar da wasu ayyuka na musamman guda uku a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da za a yi da bashin $1.57bn

1. Harkar ilimi da lafiya

Bankin Duniya ya ba gwamnatin Najeriya bashin $500m domin bunkasa harkar ilimi da kiwon lafiya a Najeriya.

Ana sa ran cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kudin wajen magance matsalolin da suka addabi ilimi da lafiya a Najeriya.

2. Lura da kiwon lafiya daga tushe

Bankin Duniya ya ba gwamnatin Najeriya bashin $570m domin gudanar da ayyukan da suka shafi kiyon lafiyar a matakin farko.

Jaridar Business Day ta wallafa cewa za a yi anfani da kudin ne domin farfaɗo da harkokin kiwon lafiya a asibitocin daga tushe.

3. Bunkasa harkokin noma

Gwamnatin Najeriya ta karbo bashin $570m domin inganta noman rani da samar da makamashi a kasar nan.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, Tinubu ya fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000

Bankin Duniya ya bayyana cewa tun daga hawa mulkin Bola Tinubu gwamnatin Najeriya ta ciwo bashin kudi har $6.52bn.

Tinubu ya fara karin albashi a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000.

Hakan na zuwa ne watanni bakwai bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashin ma'aikatan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng