Jerin Muhimman Lokuta 5 a Gwagwarmayar Samun 'Yancin kan Najeriya
- Yayin da Najeriya ke bikin cika shekara 64 da samun ƴancin kai, lokaci ne da za a yi la'akari da muhimman abubuwa da suka faru a gwagwarmayar
- Abubuwa da dama da suka haɗa da kafa ƙungiyar matasan Najeriya zuwa taro kan kundin tsarin mulki na shekarar 1958, sun taka muhimmiyar rawa
- Legit Hausa ta yi duba kan wasu fitattun abubuwa guda biyar da suka taka rawar gani wajen tabbatar da samun ƴancin kan Najeriya a shekarar 1960
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Yayin da Najeriya ke shirin bikin cika shekara 64 da samun ƴancin kai, yana da matuƙar muhimmanci a yi la'akari da muhimman lokutan da suka yi tasiri a ƙoƙarin samun ƴancin kanta.
Gwagwarmayar samun ƴancin kai cike take da jajircewa, sadaukarwa domin kaucewa mulkin mallaka.
Ga lokuta biyar da suka taka rawar gani a ƙoƙarin Najeriya na samun ƴancin cin gashin kanta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Kafa ƙungiyar matasan Najeriya (NYM) - 1934
Ƙungiyar NYM ita ce ƙungiya ta masu kishin ƙasa ta farko da aka samar a Najeriya.
Ƙungiyar da aka kafa ta a shekarar 1934, ta taka muhimmiyar rawa wajen zaburar da ƴan Nijeriya wajen nuna adawa da masu mulkin mallaka.
2. Zanga-zangar mata a Aba - 1929
Zanga-zangar da mata suka yi a Aba a shekarar 1929, zanga-zanga ce ta nuna adawa da mulkin mallaka wacce mata daga yankin Kudu maso Gabas na Najeriya suka jagoranta.
Dubunnan mata sun yi zanga-zangar nuna adawa da ƙaƙaba haraji da takurar da hukumomin mulkin mallaka na Burtaniya ke yi, cewar rahoton Pulse.ng.
Wannan zanga-zangar ta nuna ƙarfin ikon da haɗin kai yake da shi da rawar da mata suka taka wajen gwagwarmayar samun ƴancin kai.
3. Kafa jam'iyyar NCNC - 1944
Jam'iyyar NCNC da Nnamdi Azikiwe da Herbert Macaulay suka kafa, ta zama babban jigo a ƙoƙarin samun ƴancin kai.
Ta haɗa kan ƙabilu da dama da yankunan ƙasar nan a ƙarƙashin inuwar neman samun ƴancin kai.
Kamfen ɗin da NCNC ta riƙa yi tare da tattaunawa da gwamnatin Burtaniya sun taka muhimmiyar rawa wajen samun ƴancin kai.
4. Kundin tsarin mulkin Richards - 1946
Kundin tsarin mulkin Richards wanda gwamnatin mulkin mallaka ta Burtaniya ta samar, ya kawo sauyi a fagen siyasar Najeriya.
Duk da cewa bai bayar da cikakken cin gashin kai ba, ya samar da hanyar kafa gwamnatocin shiyya-shiyya da ƙara yawan ƴan Najeriya da ake damawa da su a cikin harkokin majalisa.
Wannan kundin tsarin mulkin ya samar da hanyar ci gaba da kawo sauye-sauye waɗanda a ƙarshe suka kai ga samun ƴancin kai.
5. Taron samar da kundin tsarin mulki na 1958
Taron samar da kundin tsarin mulki na shekarar 1958 da aka yi a Landan, ya kasance wani muhimmin lokaci a gwagwarmayar Najeriya wajen samun ƴancin kai.
Shugabannin Najeriya da suka haɗa da Abubakar Tafawa Balewa da Obafemi Awolowo sun tattauna da jami’an ƙasar Birtaniya domin kammala ba Najeriya ƴancin kai.
Taron ya samar da yarjejeniyar cewa Najeriya za ta zama ƙasa mai cin gashin kanta a ranar 1 ga watan Oktoba, 1960.
Gwamnatin Najeriya ta ba da hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin murnar zagayowar ranar samun ƴancin kan Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024 a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng