Bauchi: Ana Kukan babu Kudi, Gwamna Ya Tattago Aikin Gyara Fadan Sarakai 11

Bauchi: Ana Kukan babu Kudi, Gwamna Ya Tattago Aikin Gyara Fadan Sarakai 11

  • Gwamnatin Bauchi na ci gaba da inganta fadojoji sarakuna, hakimai da masu gundumomin jihar domin daga darajar masarautu
  • A wannan karon, Gwamna Bala Mohammed ya ba da umarnin a gyara fadojoji masu gunduma 11 na karamar hukumar Dass a jihar
  • A zantawarmu da Muslim Dabo Dass ya ce masu gundumomin na taka rawar wanzar da zaman lafiya don haka sun canci gyaran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da gyara tare da inganta fadojojin sarakunan gundumomi 11 na karamar hukumar Dass da ke a jihar.

Gwamnan ya kuma amince da sake gyara fadar mai martaba Sarkin Dass, Alhaji Usman Othman, a ci gaba da sauye-sauyen da ake samu a masarautun gargajiya a jihar.

Kara karanta wannan

"Kai ka jawo tsadar rayuwa": 'Dan majalisa ya cire tsoro ya fadawa Tinubu gaskiya

Gwamnatin Bauchi za ta gyara fadojojin masu gunduma 11 a Dass
Masu gunduma 11 a Dass za su rabauta da gyaran fadojojinsu daga gwamnatin Bauchi. Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Shugaban karamar hukumar Dass, Mohammed Jibo ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dass: Gwamna zai gyara fadojoji 11

Mohammed Jibo, ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar injiniyoyi a ziyarar tantance fadojojin sarakunan kauyukan 11 gabanin gyara da inganta su.

Shugaban karamar hukumar ta Dass ya yabawa Gwamna Bala Mohammed bisa kokarinsa na samarwa sarakunan jihar yanayi mai kyau na gudanar da aiki.

A cewar Mohammed Jibo, samar da muhalli mai kyau zai bunkasa ayyukan sarakunan tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga zaman lafiya da ci gaban jihar.

"Muna godiya ga gwamna" - Jibo

Shugaban karamar hukumar ya ce:

"Ci gaba da inganta fadojojin sarakuna, hakimai da masu gundumomi a jihar na daga yunkurin gwamnatin Bala Mohammed na daga darajar masarautun gargajiya.

Kara karanta wannan

'Sarkin ne mai daraja ta 1', Ganduje ya kwatanta masarautar Bichi da ta Sanusi II

“Muna godiya kwarai da gaske ga Gwamna Bala Mohammed kan yadda ya fadada gyaran fadojojin sarakunan jihar har zuwa karamar hukumar Dass.
"Gwamna yana da cikakkiyar masaniya game da irin rawar da sarakunanmu suke takawa a matsayin masu kula da al’adu da zaman lafiyar mutanensu."

"Fadojojin masu gundumar sun lalace"

A zantawarmu da Muslim Dabo Dass, ya ce fadojoji masu gundumar 11 da za a gyara sun dade da lalacewa, wanda duk wanda ya gansu zai iya dauka cewa ba na masu sarauta ba ne.

Muslim Dass ya ce masu gundumar garin sun kasance suna taka rawa a matsayin masu kula da al’adu da zaman lafiyar mutanen yankin.

"Duk da cewa akwai sauran ayyuka a gaba, amma gyara fadojojin masu littattafan na da fa'ida sosai. Suna fadi tashin ganin an samu zaman lafiya a fadin Dass."

- A cewar Muslim.

Gwamna ya nada sabon sarki

A wani labarin mun ruwaito cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sanar da nada sabon sarkin Ningi na 17 bayan rasuwar Alhaji Yunusa Danyaya.

Kara karanta wannan

Cin hancin N15m: Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban EFCC da wasu mutum 2

A cikin wata sanarwa daga gwamnatin jihar, Gwamna Bala ya amince da nadin Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon sarkin Ningi domin ya gaji mahaifinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.