Ana Zargin an Dauki Hayar 'Yan Bindiga, Sun Kashe Dan Takarar PDP a Kaduna
- Miyagun yan bindiga sun kashe dan takarar kansila a jihar Kaduna tare da kaninsa a hanyarsu ta komawa gida
- Ana zargin harin ba ya rasa nasaba da siyasa, domin ya na dawowa daga yawon yakin neman zabe ne lamarin ya auku
- Shugaban karamar hukumar Kauru a jihar ne ya tabbatar da kisan Raymond Timothy da kaninsa James Timothy
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Wasu yan bindiga sun kashe dan takarar kansila a mazabar Pari, a karamar hukumar Kauru, a jihar Kaduna Raymond Timothy.
Shugaban karamar hukumar, Barnabas Chawai ne ya tabbatar da kisan, inda ya ce an kashe kansilan tare da kaninsa James Timothy.
A labarin da ya kebanta da Punch zuwa yanzu, an samu tabbacin yan bindiga sun kashe dan takarar kansilan da dan uwansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne suna kan babur a hanyarsu ta dawowa daga yakin neman zabe.
Ana zargin kisan siyasa a Kaduna
Shugaban karamar hukumar Kauru a Kaduna, Barnabas Chawai ya yi zargin kisan dan takarar kansila a yankin, Raymond Timothy ba ya rasa nasaba da siyasa.
Marigayin dan takarar ya bar mace daya da yara uku, kuma matarsa na da juna biyu - ana sa ran za ta haifi na hudu a kwanan nan.
Kisan Kaduna: An nemi daukin yan sanda
An nemi yan sanda su gaggauta daukar mataki kan kisan dan takarar kansila a mazabar Pari da ke karamar hukumar Kauru a Kaduna.
Bayan zargin kisan na da alaka da siyasa, shugaban karamar hukumar, Hon. Chawai ya bukaci jami'an tsaro su sanya matakan dakile irin wannan kisan a gaba.
'Yan bindiga sun sace shugaban NURTW a Kaduna
A baya mun wallafa cewa wasu yan ta'adda sun sace shugaban NURTW a kauyen Kidandan a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna karo na biyu.
An sace shugaban ne bayan ya kubuta daga hannun miyagun yan ta'adda inda ya shafe kwanakin 60, amma a wannan jikon, an kwashe shi da yaran makwabtansa guda uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng