Bidiyo: Kashim Shettima Ya Dawo Najeriya daga Kasar Amurka, Zai Gana da Tinubu
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya dawo Najeriya daga taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) da ya halartar a Amurka
- Mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai a ofishin mataimakin shugaban kasar, Stanley Nkwocha ya sanar da hakan ranar Lahadi
- An rahoto cewa Shettima zai gana da Shugaba Bola Tinubu a inda ake gudanar da bubukuwa na murnar cikar Najeriya shekaru 64 da 'yanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya iso birnin Abuja bayan kammala taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.
A ranar Lahadi ne Shettima ya dawo Najeriya bayan wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen taron UNGA na 79 da aka kammala a Amurka.
Shettima ya dawo Najeriya daga Amurka
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha ya bayyana haka a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar Nkwocha ta ce:
"A ranar Lahadi ne mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya dawo Abuja bayan samun nasarar wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da aka kammala a birnin New York na kasar Amurka.
"Mataimakin shugaban kasar, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya kuma gabatar da bayanin a madadin Najeriya a babban taron."
Shettima zai gana da Shugaba Tinubu
Sanarwar ta kuma ce Shettima ya gudanar da tarurruka da dama da wasu kasashe da kuma sauran abubuwa da suka faru a gefen babban taron.
Bayan isowarsa kasar, sanarwar ta ce Shettima zai:
"Zai hadu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin gudanar da wasu bukukuwa da aka hada a wani bangare na bikin murnar cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai."
Tinubu ya fasa zuwa taron UNGA
Tun da fari, mun ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 za a gudanar a birnin New York ba.
Fadar ta ce Tinubu na so ya mayar da hankali kan al'amuran cikin gida da magance wasu kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman bayan ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar.
Asali: Legit.ng